Da safiyar yau Lahadi ne jirgin kasa mai matukar sauri, mai lamba G3998, ya tashi daga tashar Ruijin zuwa birnin Yan’an, sassa biyu masu matukar muhimmanci dangane da doguwar tafiyar da sojojin juyin juya hali na Sin ko “Red Army” suka gudanar a tarihi.
Wannan ne karon farko da jirgin kasa mai matukar sauri ya hade sassan biyu, inda nisan tafiyar ya kai kusan kilomita 1850, tare da ratsa lardunan Jiangxi, da Hubei da Shaanxi cikin kusan sa’o’i 11 da mintuna 32, kana kan hanyar ana iya ganin tarin ababen kashe kwarkwatar idanu na halittu da al’adun yawon bude ido.
A bana ne ake cika shekaru 90 da cimma nasarar doguwar tafiyar da dakarun na “Red Army” na Sin suka gudanar. Kuma biranen Ruijin da Yan’an, su ne mafiya muhimmanci a batun doguwar tafiyar, kama daga mafari zuwa muhimmiyar cibiyar juyin-juya-hali ta JKS. Kazalika, yankunan biyu suna bangaren gabashi da arewa maso yammacin kasar Sin. (Saminu Alhassan)














