ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ma’aikatan FCT Sun Fara Yajin Aiki, Sun Rufe Ofisoshin FCTA Da FCDA

by Abubakar Sulaiman
8 months ago
FCT

Ofisoshin babban shalƙwatar Hukumar Gudanar da Birnin Tarayya (FCTA) da Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCDA) sun kasance babu kowa a kulle a safiyar Litinin, yayin da ma’aikata suka amsa kiran yajin aiki na har sai bana ta gani da Kwamitin Hadin Gwuiwar Kungiyoyin Ma’aikata (JUAC) suka bayar kan buƙatar inganta yanayin aiki.

Da misalin ƙarfe 8:00 na safe, an kulle manyan kofofin shalƙwatar, inda ma’aikata da masu ziyara suka kasa shiga. Wannan mataki ya biyo bayan wata sanarwa da JUAC ta fitar a daren Lahadi mai taken “Code Remain at Home”, wadda ta umarci cikakken biyayya ga yajin aikin.

Sanarwar ta ce: “Dukkan ma’aikata an shawarce su da su zauna a gida yayin da JUAC ta fara yajin aiki. Kada ku zo wurin aiki saboda jami’an JUAC za su kasance a wurin don tabbatar da bin wannan umarni. Aluta Continua! Victoria Acerta! Yaki yana ci gaba, nasara tabbatacciya ce!”

ADVERTISEMENT

Wani jami’in JUAC da ya yi magana bisa sharaɗin ɓoye sunansa ya bayyana yajin aikin a matsayin matakin ƙarshe. Ya ce: “An matse mu sosai. Ƙorafinmu na neman ingantaccen yanayin aiki a FCTA ba a kula da shi ba tsawon lokaci. Ya isa! Za mu ci gaba da zama a gida har sai an magance koke-kokenmu.”

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

Ziyara zuwa hedikwatar ta tabbatar da dakatar da dukkan ayyuka, yayin da jami’an kungiya ke sintiri a kofofi kuma babu wani aiki na gudanarwa a ciki. Duk da cewa cikakken bayanin bukatun ma’aikatan bai fito fili ba tukuna, majiyoyin kungiyar sun ce sun shafi batutuwan walwalar ma’aikata, yanayin aiki, da kuma aiwatar da hakkokin da aka dade an amince da su.

A halin yanzu, shugabannin FCTA da FCDA ba su fitar da wani bayani kan yajin aikin ba, lamarin da ya kara jefa mazauna birnin cikin damuwa. Wannan yajin aiki ya janyo babban tashin hankali a harkokin gudanarwa da ayyuka a Birnin Tarayya, inda babu wani alamar lokacin da za a fara tattaunawa don warware matsalar.

FCT
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Next Post
Gwamnatin Kano Zata Kashe Biliyan ₦8.53bn Wajen Aiwatar Da Wasu Aiyuka

Gwamnatin Kano Zata Kashe Biliyan ₦8.53bn Wajen Aiwatar Da Wasu Aiyuka

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.