Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya soki matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur, inda ya bayyana matakin a matsayin rashin hankali.
Ya kuma buƙaci ’yan Nijeriya da su ƙi zaɓen Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.
Amaechi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taro da jam’iyyar ADC ta gudanar a Jihar Edo.
Ya zargi manufofin tattalin arziƙin gwamnatin Tinubu da ƙara tsananta talakawa a ƙasar.
“Mahaukaci ne kawai zai zaɓi Tinubu,” in ji shi, inda ya bayyana yadda ’yan Nijeriya ke fama da wahalhalun rayuwa.
Amaechi ya ƙi amincewa da iƙirarin Tinubu cewa cire tallafin man fetur mataki ne da ya zama dole.
Ya ce matakin ya nuna rashin tunani ne, musamman ganin cewa an shawarci shugaban ƙasar da ka da ya ɗauki wannan mataki.
Tsohon ministan ya kuma soki yadda Nijeriya ta kasa amfani da albarkatun man fetur da iskar gas da ta ke da su wajen bunƙasa masana’antu da inganta rayuwar al’umma.
Amaechi ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, zai samar da tallafi ga masana’antun cikin gida domin ƙara yawan kayayyakin da ake samarwa a Nijeriya da kuma rage matsin tattalin arziƙi ga ’yan ƙasar idan aka zaɓe shi a 2027.














