Kakakin Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, Mohammed Sani Haruna, ya bayyana cewa zaɓin Jihar Kaduna domin kaddamar da yaƙin neman zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shekarar 2027 wata alama ce ta nasarar da yake hasashen shugaban zai samu a zaɓen mai zuwa.
Mohammed Sani Haruna ya bayyana hakan ne a taron manema labarai Yayin Kaddamar da cibiyar tattara bayyanai dangane da shirye-shiryen jam’iyyar na karɓar Shugaba Tinubu a Jihar Kaduna, inda ya nuna cewa APC na ganin jihar a matsayin muhimmiyar cibiyar siyasa a Arewacin Nijeriya.
Ya ce ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani, APC a Kaduna na da ƙarfin siyasa da ya sa yake ganin babu wani ɗan takarar adawa da zai iya yin gogayya da Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
Kakakin jam’iyyar ya bayyana cewa wannan matsayi nasa ya samo asali ne daga yadda yake kallon ƙarfin jam’iyyar da kuma yadda shugabanninta ke gudanar da harkokinsu a jihar.
Ya ƙara da cewa APC ta fara ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da nasarar shirye-shiryen tarbar Shugaba Tinubu da ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a Kaduna.
A cewarsa, tuni aka ƙaddamar da wani ofishin tattara bayanai domin taimakawa wajen tsara shirye-shiryen zuwan shugaban ƙasa da kuma daidaita ayyukan masu ruwa da tsaki.
Mohammed Sani Haruna ya ce ofishin zai taimaka wajen tattara bayanai da suka shafi shirye-shiryen taron, tare da sauƙaƙa sadarwa tsakanin waɗanda ke da hannu a cikin shirye-shiryen.
Ya kuma bayyana cewa ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen a Kaduna na da muhimmanci ga APC, la’akari da matsayin jihar a siyasar Arewa da kuma yawan al’ummar da take da su.
A cewarsa, jam’iyyar na ci gaba da shirye-shirye domin ganin an gudanar da taron cikin tsari, tare da haɗa kan magoya baya da shugabannin APC daga sassa daban-daban na jihar.














