ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Kwalejin Koyar Da Ƙwararrun Ma’aikatan Jinya A Rigasa

by Shehu Yahaya
1 week ago
Uba sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sanya hannu kan dokar kafa Kwalejin Koyar da Ƙwararrun Ma’aikatan Jinya a Matakin Farko a Rigasa, domin ƙara samar da ƙwararrun ma’aikatan lafiya a jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar..

Ya ce kafa kwalejin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin magance ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan jinya, tare da inganta ayyukan kiwon lafiya a faɗin jihar.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, makarantar za ta taimaka wajen horas da ma’aikatan jinya a fannoni na musamman, musamman waɗanda suka shafi kula da mata masu juna biyu, jarirai da yara, bayar da agajin gaggawa da kuma kula da marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali.

Sanarwar ta bayyana cewa, ƙarƙashin dokar kafa kwalejin ta shekarar 2026, makarantar za ta kasance cibiyar horas da ƙwararrun ma’aikatan jinya a matakin manyan makarantu, inda babban harabarta zai kasance a Rigasa.

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Dokar ta kuma tanadi yiwuwar buɗe wasu harabobi, makarantu da cibiyoyin horaswa a wasu wurare, matuƙar hukumomin da abin ya shafa sun amince da hakan.

Kwamishinan ya bayyana cewa kwalejin za ta koyar da fannoni daban-daban da suka haɗa da ungozoma, kula da lafiyar kwakwalwa, aikin jinya a lokacin tiyata, kula da lafiyar yara, bayar da agajin gaggawa, kula da marasa lafiya a sashen kulawa ta musamman, kiwon lafiyar jama’a, da kuma koyarwa da gudanar da harkokin jinya.

Ya ƙara da cewa kafa makarantar zai taimaka wajen haɓaka ƙwarewar ma’aikatan lafiya, ƙarfafa bincike da nazari, da kuma samar da damarmakin ci gaba da horaswa ga ma’aikatan jinya.

Haka kuma, kwalejin za ta yi aiki tare da asibitocin koyarwa, jami’o’i, cibiyoyin kula da marasa lafiya na musamman da sauran cibiyoyin horaswa da aka amince da su.

A cewar sanarwar, dokar ta tanadi kafa Majalisar Gudanarwa da za ta kula da tsare-tsaren makarantar, da kuma Hukumar Ilimi wadda za ta kasance mai kula da ingancin karatu, bincike da horas da ɗalibai.

Dukkan shirye-shiryen karatun kwalejin za su kasance ƙarƙashin ƙa’idoji da tsarin tantance ingancin karatu na Hukumar Kula da Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Nijeriya (NMCN), da sauran hukumomin da doka ta ba su ikon gudanar da irin wannan aiki.

Maiyaki ya ce kafa kwalejin ya yi daidai da manyan tsare-tsaren gwamnatin Gwamna Uba Sani na sake fasalin ɓangaren kiwon lafiya, waɗanda suka haɗa da inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 255 da gyaran manyan asibitoci 16 a faɗin jihar.

Ya jaddada cewa, samar da gine-ginen kiwon lafiya kaɗai bai isa ba, sai an samar da ƙwararrun ma’aikata waɗanda za su iya gudanar da ayyukan lafiya yadda ya kamata, musamman a yankunan da ba su da isassun ma’aikatan lafiya.

Kwamishinan ya ƙara da cewa kwalejin za ta taimaka wajen samar da ɗorewar tsarin horas da ƙwararrun ma’aikatan jinya, ƙarfafa cibiyoyin kiwon lafiya da inganta kulawa da marasa lafiya a jihar.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta yi ƙoƙarin bunƙasa makarantar domin ta zama cibiyar ƙwarewa wajen koyarwa, bincike da horas da ma’aikatan jinya, tare da taimakawa wajen tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Jihar Kaduna.

Uba sani
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Kotu Ta Ba Da Belin Ƴar Jarida Farida Isiak Bayan Tsare Ta A Kaduna
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Majalisar Malamai Ta Ƙasa Ta Buƙaci Gwamnati Ta Yi Wa El-Rufai Da Sheikh Sani Zaria Adalci
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    NAPTIP Ta Buƙaci ‘Yan Jarida Su Ƙara Bincike Wajen Bayar Da Rahotannin Cin Zarafin Mata
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    2027: Kaddamar da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna Alamar Nasarar Tinubu Ce A 2027 —Kakakin APC

MASU ALAKA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya
Labarai

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya
Ra'ayi Riga

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026
Next Post
Za A Wallafa Makalar Shugaba Xi Game Da Bunkasa Tsarin Jagorancin Jamiyyar Kwaminis Ta Sin

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.