Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu Dan Musa, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na biyan malaman addini 7,525 alawus-alawus duk wata domin su rika wa’azi kan zaman lafiya, kwanciyar hankali da zaman tare a matsayin wani ɓangare na magance matsalar ‘yan bindiga da sauran ƙalubalen tsaro a jihar.
Da yake magana a wata hira da LEADERSHIP Sunday, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta fahimci muhimmiyar rawar da malaman addini ke takawa wajen tasiri ga al’umma da kuma inganta zaman lafiya tsakanin jama’a.
Ya ce, “Mun fahimci muhimmancin addini wajen magance kalubalen tsaro. A lokaci guda, mun dauki malaman addini aiki tare da sanya su cikin tsarin biyan alawus na wata-wata. Akwai mutum 7,525 daga cikinsu da ake biyansu domin su riƙa wa’azi kan zaman lafiya, kwanciyar hankali da zaman tare.”
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta rungumi matakan yaki da ‘yan bindiga da kuma matakan da ba na yaki ba wajen tunkarar matsalar rashin tsaro, yana mai cewa kalubalen tsaro a jihar na bukatar fiye da amfani da jami’an tsaro masu ɗamara.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta dauki masu unguwanni 6,662 aiki, wadanda ake biyansu alawus na wata-wata, a wani ɓangare na kokarin ƙarfafa samun bayanan sirri daga al’umma da kuma kara shigar da jama’a wajen tabbatar da zaman lafiya.














