Wasu mutanen Japan na daukar sabbin matakai masu cike da wayo da nufin jirkita tarihi. Bisa labarin da aka bayar kwanan nan, an ce, masu ra’ayin rikau na Japan na baiwa manyan tsarukan fasahar AI na duniya bayanai na jabu kan tarihin yakin duniya na 2, don tsarukan su rika fitar da amsoshi masu dauke da ra’ayoyin da ba su dace ba game da tarihi in an yi musu tambaya, inda suka bayyana harin da Japan ta kaiwa Sin a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1937 don yunkurin mamaye Sin a matsayin “Rikicin Soji Tsakanin Japan da Sin”, tare da bayyana “kisan kiyashin da sojojin Japan suka aikata a birnin Nanjing” a matsayin “Cin tura da Sin ta yi a Nanjing”. Har ila yau, sun gyara zaluncin mamayar da Japan ta yi wa yankin kudu maso gabashin Asiya a matsayin “Kula da Albarkatun yankunan kudu da Japan ta yi ”.
Daga gurbata littattafan tarihi, zuwa kirkirar bidiyon karya na fasahar AI, zuwa sanya guba cikin bayanai, masu ra’ayin rikau na Japan na ci gaba da yunkurin kirkirar sabbin hanyoyi don wanke tarihin mamayar da ta dade tana gudanarwa. Ba shakka, masu ra’ayin rikau na Japan ke aikata zambar ne don taimaka wa gwamnatin kasar wajen “farfado da karfin soja a Japan”, wanda hakan ya kara mai da “sabon salon ra’ayin nuna karfin soja” ya zama barazana ga duniya. (Amina Xu)














