Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya isa Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar Talata domin ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi masa kan zargin cin hanci da rashawa, tare da dan takarar gwamnan ADC, Isa Ashiru.
El-Rufai ya isa kotun da misalin karfe 11:50 na safe, gabanin lokacin sauraron karar da aka tsara, yayin da jami’an tsaro suka tsaurara matakan tsaro a harabar kotun.
A zaman kotun da ya gabata, Mai Shari’a Darius Khobo ya umarci hukumar ICPC da ta kawo El-Rufai kotu bayan tsohon gwamnan bai halarci zaman ranar Litinin ba saboda bukatar ganin likitansa.
Wannan zaman ya zo ne kwanaki kadan bayan Kotun Daukaka Kara da ke Kaduna ta yi watsi da karar El-Rufai kan kin amincewa da bukatarsa ta beli.
Tun ranar 18 ga Fabrairu, 2026, El-Rufai yake tsare a hannun ICPC kan zarge-zargen da suka shafi almundahanar kudi da sauran laifukan da ake dangantawa da mulkinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Tsohon gwamnan ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su, kuma ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa. Har yanzu dai zarge-zargen suna gaban kotu domin yanke hukunci.













