Nijeriya, kamar dai sauran wasu kasashen Afrika dama duniya gaba daya na fuskantar barnar da matsananciyar ambaliyar ruwa da ta haifar ta asarar rayuka da dimbin dukiyar miliyoyin Nairori.
Abubuwan da suka hada da ruwa kamar da bakin kwarya da matsalolin da suka shafi dumamar yanayi wanda gwamnati ta kasa daukar matakin da ya kamata don dakilewa ya sanya duk kokarin da ake yi na shawo kan ambaliyar ya ci tura.
A kan haka a duk shekara barnar da ambaliyar ke haifarwa yake kara munana. Abin takaicin kuma a nan shi ne yadda gwamnati bata mayar da hankali ga matakan dakile yawaitar ambaliyar da irin barnar da take haifarwa ba a duk shekara. Ya zuwa watan Satumba ambaliyar ta yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyin al’umma da amna duk kuwa da gargadin da aka yi aukuwar lamarin.
A ranar 19 ga watan Satumba, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA) ta yi gargadin yiyuwar ambaliya daga Tafkin Kogin Neja da Benuwa zuwa wasu jihohi 14 a fadin tarayyar Nijeriya.
Hukumar NEMA ta bayar da gargadin ne tare da hadin gwiwar Hukumar Hasashen Yanayi ta Kasa inda ta bayyana yiyuwar gaggarumin ambaliyar ruwa a jihohin Adamawa, Taraba, Benuwai, Neja, Nasarawa, Kebbi, Kogi, Neja, Delta, Edo, Delta, Anambra, Cross Riber, Ribers da kuma Jihar Bayelsa.
A taron da ya yi da manema labarai, Shugababn Hukumar NEMA, Mustapha Habib Ahmed, ya bukaci gwamnatin wadannan jihohin su gaggauta tayar da al’ummar da ke a yankuna da suka fi fuskantar hatsari ambaliyar zuwa yankunan da bashi da matsala don kaucewa asarar rayuka da dukiya.
Ya bayar da bayanin irin tsananin da lamarin za iya yi, yana mai cewa, masu kula da babban dam din nan na kasar Kamaru mai suna Lagdo dam sun fara sake ruwa tun daga ranar 14 ga watan Satumba 2022.
“Muna sane da an fara sake ruwa daga wannan Dam zuwa yankuna Nijeriya ta kogin Benuwai wanda hakan zai kai ga samuwar ambaliyar ruwa a garuruwa da dama tare da haifar da barna mai yawa.
“Wannan ruwa da aka sako zai kara ta’azzara matsalar da ake fusksanta a wasu Dam-dama na Nijeriya kamar na Kainji, Jebba da Shiroro wadanda suma ana sa ran za su yi ambaliya, kamar dai yadda hukumar kula da yanayi ta yi hasashe.”
Ganin muhimmanci da girman matsalar da ake fuskanta sai ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su gaggauta daukar matakin da ya kamata na kawar da al’ummar yankunan da ambaliyar zai fii shafa da gaggawa.
Ba wai ba a taba ganin irin wannan lamarin ba ne amma dai ba a taba ganin irin yadda lamarin ya gawurta ba kamar a wannan lokacin. Bayani ya nuna cewa, mutum 805 suka mutu a sassan Nijeriya a shekarar 2017 da 2022, kamar yadda bayanai daga hukumar Bayar da Agajinn Gaggawa ya nuna da kuma kafar Floodlist kafar da ke bayar da bayanai na labaran da suka shafi ambaliyar ruwa a sassan duniya.
Zuwa yanzu ambaliyar ta tarwatsa mazauna 1,290,455 kamar yadda bayanai ya nuna, hukumar NEMA ta kuma sanar da cewa, mutum 372 ne suka mutu sakamakon ambaliyar a shekarar 2022, yayin ambaliyar ta shafi mutum fiye da 508,000 yayin da mutum 277 suka ji munanan raunuka a cikin wata 8 da suka wuce.
Tabbas wannan na kara nuna irin girmar mastalar da ake fuskanta ne, ya bayyana lamarin inda yake cewa, duniya na fuskantar babbar matsala, matsala daga abubuwan da suka shafi dumamar yanayi. Watakila in har abubuwan da suka faru a cikin watannin uku basu isa su gamsar da mutum akan irin matsalar da duniya ke ciki ba to lallai babu wani abin da ya isa ya gamsar da shi game al’amarin dumamar yanayi.
Tun daga ambaliyar da ta taso daga kasar Pakistan da ambaliyar nan mai tayar da hankali ta ‘Ian’ data ratsa Florida zuwa Carolina ta Yamma a kasar Amurka a bayyana yake cewa lallai abubuwa ba kamar yadda suke ba ne a da a halin yanzu.
Lamarin bai bar yankin Turai ba suma sun dandana barnar ambaliyar tun daga Landan har zuwa Spaniya duk sun fuskanci barnar ambaliyar a cikin wannan shekara haka ma a yankin nahiyar Asia inda kasar Chana ta fusknaci matsananciyar yanayi irn wanda basu taba fuskanta ba a a tsawon shekaru masu yawa.
A tsawon shekaru, hujjoji na cutar da muhalli sun bayyana a Ni.