Matasa huɗu daga ƙauyen Tsangai, da ke gundumar Moyori a ƙaramar hukumar Yusufari ta Jihar Yobe, sun mutu a ƙasar Algeria yayin da suke neman abin dogaro da kai.
Shugaban ƙaramar hukumar Yusufari, Adam Jibrin, ne ya tabbatar da mutuwar matasan a cikin saƙon ta’aziyyar da ya fitar.
Jibrin ya ce mutuwar matasan ta jefa iyalansu da al’ummar Yusufari cikin jimami.
Ya bayyana cewa matasan sun tafi Algeria ne domin neman ingantacciyar rayuwa da damar samun abin dogaro da kai don rufa wa iyalansu asiri.
Shugaban ya jajanta wa iyalan mamatan, ’yan uwa da abokansu, tare da roƙon Allah Ya gafarta musu kuma Ya ba iyalansu ƙarfin jure wannan babban rashi.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya kare matasan Nijeriya da ke tafiya ƙasashen waje domin neman abun dogaro da kai.














