Kamfanin Dangote ya buɗe sayar da sabbin hannayen jarinsa na farko (IPO) na Matatar Mai ta Dangote, wanda darajarsa ta kai Naira tiriliyan 2.15, a Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya (NGX).
Shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ne ya kaɗa kararrawar kasuwa a ranar Litinin a filin cinikin NGX da ke Legas, lamarin da ya sanya Matatar Dangote ta zama matatar mai ta farko da aka gabatar wa masu zuba jari a kasuwar hannayen jarin Nijeriya cikin tarihin shekaru 66 na NGX.
IPO ɗin ya ƙunshi sabbin hannayen jari guda biliyan 4.1, inda ake sayar da kowane kaso a kan Naira 525. Mafi ƙarancin adadin da mutum zai iya saya.
An buɗe sayar da hannayen jarin ne a ranar 14 ga Satumba, 2026, kuma ana sa ran rufe sayarwar a ranar 13 ga Oktoba, 2026, bisa sharuɗɗan da ke cikin takardar IPO.
Kamfanin ya ce sayar da hannayen jarin zai bai wa ƙananan masu zuba jari, manyan cibiyoyi da masu zuba jari da suka cancanta daga Afirka damar mallakar wani kaso a cikin matatar.













