Ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN), reshen Jihar Kaduna, ta ce makiyaya sun rasa sama da shanu 200,000 tsakanin Janairu zuwa Satumban 2026 sakamakon satar shanu, da hare-haren ’yan bindiga, da rikicin manoma da makiyaya da sauran matsalolin tsaro.
Shugaban MACBAN na Jihar Kaduna, Alhaji Abdulhamid Musa Albarka, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna. Ya kuma ce an kashe akalla mambobin ƙungiyar 50 a cikin wannan lokaci, inda ya danganta da rikice-rikicen al’umma, da hare-haren manoma da kuma kisan da ’yan bindiga ke yi yayin satar shanu.
Ƙungiyar ta ce asarar shanun ta jefa iyalai da dama cikin matsanancin talauci, ganin cewa kiwon dabbobi shi ne babbar hanyar samun abin dogaro ga yawancin makiyayan da abin ya shafa. Ta bayyana Kachia, da Chikun, da Kagarko, da Giwa, da Igabi, da Jama’a, da Kaura, da Sanga, da Jaba, da Kudan, da Makarfi, da Lere, da Zangon Kataf da Kauru a matsayin wasu daga cikin wuraren da matsalar ta fi shafa.
MACBAN ta kuma nuna damuwa kan kasuwar dabbobi ta Rijana da ke Ƙaramar Hukumar Kachia, tana mai kira ga gwamnati da jami’an tsaro su tabbatar da cewa ba a amfani da kasuwar wajen sayar da dabbobin da aka sace. Sai dai ta jaddada cewa ba ta zargi dukkan ’yan kasuwa ko masu dabbobi da ke kasuwar da hannu a aikata laifi ba.
Ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin tsaro da su ƙara ayyukan leƙen asiri da samame a wuraren da ake yawan satar shanu, tare da samar da hanyoyin gano da dawo da dabbobin da aka sace ga masu su. Ta kuma buƙaci a kafa kwamiti da zai tantance yawan dabbobin da aka rasa da iyalan da matsalar ta shafa.














