Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa hare-haren Boko Haram sun lalata gine-ginen makarantu sama da 5,000 a lokacin da rikicin ya tsananta, lamarin da ya jefa yara kimanin miliyan 2.2 cikin rashin zuwa makaranta.
Daily trust ta rahoto cewa, Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, lokacin da Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi A. Sule, ya kaddamar da wasu ayyukan raya kasa a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Daga cikin ayyukan da aka kaddamar akwai gadar sama ta Post Office, Makarantar Sakandare ta yankin Larawaram, Makarantar Firamare da Sakandaren Shehu Sanda Kyarimi I, da kuma hanyar kilomita 2.5 da aka mayar ta zama mai layuka biyu, tare da magudanan ruwa masu tsawon kilomita biyar daga mahaɗar Budum Tandari zuwa Kasuwan Shanu.
Zulum ya ce illar da rikicin Boko Haram ya haifar ba ta tsaya kan lalata gine-ginen makarantu kadai ba, domin malamai da masu kula da makarantu da dama sun rasa rayukansu yayin da suke gudanar da ayyukansu.
Sai dai gwamnan ya jaddada cewa matakan da gwamnatinsa ke dauka sun wuce aikin sake gina gine-ginen makarantu da aka lalata.Ya ce manufar gwamnatin ita ce dawo da damar samun ilimi, sake gina kwarin gwiwar al’umma da kuma samar wa yara damar samun kyakkyawar makoma.
“Gina makarantu ba wai kawai batun sake gina gine-gine ba ne. Abu ne da ya shafi dawo da damar samun ilimi, sake gina kwarin gwiwar al’umma, da samar wa yaranmu damar samun kyakkyawar makoma,” in ji Zulum.














