ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Malamai Da Limamai 3,000 Sun Yi Addu’ar Zaman Lafiya Da Nasarar Tinubu A 2027

by Hussein Yero
47 minutes ago

Kimanin malamai da limamai 3,000 daga ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara sun gudanar da addu’a ta musamman domin samun dawwamammen zaman lafiya a jihar da Nijeriya baki ɗaya, tare da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’ar samun nasara a zaɓen 2027.

An gudanar da addu’ar ne a gidan Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen Tinubu, Sanata Abdul’aziz Yari.

Addu’ar ta kuma mayar da hankali kan sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro da ke yaƙi da rashin tsaro, inda aka roƙi Allah Ya kare su, Ya ba su ƙarfi da nasara wajen fatattakar ’yan ta’adda da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar. Malaman sun kuma yi addu’ar a gudanar da zaɓen 2027 cikin lumana ba tare da rikici ba.

ADVERTISEMENT

Daga cikin manyan malaman da suka jagoranci addu’ar akwai Sheikh Liman Dan Alhaji daga Babban Masallacin Gusau, wanda ya roƙi Allah Ya sa zaɓen 2027 ya gudana lafiya. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ƙara wa jami’an tsaro ƙarfi wajen dakile duk wani yunƙuri na haddasa rikicin siyasa ko na addini a lokacin zaɓen.

Haka kuma, Sheikh Sadiqu Saddeeq ya yi wa Sanata Yari addu’ar samun nasara wajen gudanar da aikin da Shugaba Tinubu ya ba shi na jagorantar yaƙin neman zaɓen dawowarsa karo na biyu. Ya ce al’ummar Zamfara masu kishin jihar su fahimci cewa aikin babban ƙalubale ne da ya shafi Sanata Yari da kuma jihar baki ɗaya, yana mai cewa: “Dukan idanu yanzu suna kan Sanata Yari.”

LABARAI MASU NASABA

An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

A nasa jawabin, Sanata Yari ya roƙi malamai da limamai su ci gaba da wayar da kan al’umma a masallatan Juma’a kan ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi wajen magance matsalar tsaro. Ya ce gwamnati na da babban shiri na tura ƙarin sojoji da za su yi aiki a Jihar Zamfara domin magance matsalar tsaro cikin gaggawa. Ya kuma tabbatar da cewa za a ƙara samar da kayan aiki ga jami’an tsaro a jihar da Nijeriya baki ɗaya.

Hussein Yero
+ postsBio
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Tsaro: Gwamna Lawal Ya Jaddada Kudirin Yaki da ‘Yan Ta’adda Ba Tare Da Sulhu Ba
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Yaƙi Da Ta’addanci: Gwamnan Zamfara Ya Jinjina Wa Jami’an Tsaro Bisa Ƙwato Ɗarurruwan Shanu
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    ’Yan Bindiga Sun Sace Dattawan Zamfara 50 Yayin Taron Sulhu A Cikin Daji
  • Hussein Yero
    https://hausa.leadership.ng/author/hussein-yero/
    Ɗan Takarar Sanata A Zamfara Ya Koka Kan Yi Wa Rayuwarsa Barazana

MASU ALAKA

An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya
Labarai

An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

September 13, 2026
Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-rufa’i
Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

September 13, 2026
Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola
Manyan Labarai

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Next Post
Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

September 13, 2026

Malamai Da Limamai 3,000 Sun Yi Addu’ar Zaman Lafiya Da Nasarar Tinubu A 2027

September 13, 2026
An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

September 13, 2026
Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

September 13, 2026

An Gudanar Da Sallar Zana’idar Tsohon Gwamnan Gongola

September 13, 2026
Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-rufa’i

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

September 13, 2026
Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

September 13, 2026
Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba

Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba

September 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.