ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Da Ke Haifar Da Fitsari Mai Kumfa (Foamy Urine)

by Sani Anwar
3 weeks ago
Fitsari

Mutane kan yi tambaya a kan abin da ke haifar da matsalar fitsari mai kumfa. Kafin sanin dalilin, ya kamata fahimci yadda fitsarin yake:

Fitsari ya ƙunshi wasu ƴan ƙananan tarkacen ƙazanta, waɗanda Ƙoda (kidney) ke tacewa; sannan ta fitar da su daga cikin jini sakamakon ayyukan da jiki ke yi.

Ƙananan tarkacen ƙazantar da ke cikin fitsarin lafiyayen mutum sun haɗa da:

ADVERTISEMENT

1- Ruwa kashi 95 cikin 100.

2- Sinadarin ‘urea’ 9.3 g/l.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

3- Sinadarin ‘chloride’ 1.87 g/L.

4- Sinadarin ‘sodium’ 1.17 g/L.

5. Sinadarin ‘potassium’ 0.75 g/L.

6. Sinadarin ‘creatinine’ 0.67 g/L.

7. Sinadarin ‘ammonia 30 micromole/L.

8. Tarkace mai launin ruwan ƙwai, wanda ke samuwa ta hanyar lalacewar ƙwayoyin jini (pigmented products of blood breakdown).

Kazalika, idan mutum na da matsalar rashin lafiya; yawan sinadarin da aka lissafa a sama; zai kasance adadinsu ya fi haka ko ƙasa da haka a cikin fitsarinsa. Sannan kuma, za a iya samun ƙarin sinadarai a cikin fitsarin nasa ko kuma yanayin fitsarin ya zama kamar haka:

1- Sinadarin ‘protein’ (proteinuria).

2- Sinadarin ‘glucose’ (sugar).

3- Ƙwayoyin jini (hematuria).

4- Rashin iya yin fitsari mai yawa (oliguria).

5- Yin fitsari mai yawan da ya wuce ƙima (polyuria).

6- Jin zafi lokacin yin fitsari (dysuria).

Abubuwan Da Ke Haddasa Fitsari Mai Kumfa (Causes of foramy urine):

Fitsari mai kumfa ya kasu gida biyu; akwai mai matsala, akwai kuma mara matsala.

Fitsari mara matsala na faruwa ne idan:

1- Mutum ya riƙe fitsarinsa na wani tsawon lokaci ba tare da ya je ya yi ba, alhali kuma ya matse shi.

2- Yayin da mutum ke sakin fitsarinsa yana fita da ƙarfi sosai. Hakan zai sa a ga kamar kumfa na tashi; sakamakon ƙarfin fitar fitsarin.

3- Yin fitsarin a wurin da aka wanke da sinadarin wanki (detergent) ko sabulu (soap) ko kuma sauran sinadarai masu kumfa na wanke banɗaki. Ragowar kumfar sinadarin, idan ya haɗu da fitsari, zai samar da kumfa ta yadda za a ga kamar fitsarin ne ke da kumfar.

4. Ya kasance mutum ba ya shan ruwa sosai (dehydration), akwai yiwuwar fitsarinsa ya zama mai kauri (concentrated).

Hakan zai sa fitsarin nasa ya yi kumfa.

5- Ɗaukar tsawon lokaci ana amfani da wasu magunguna na kashe raɗaɗi ko rage kumburi ko zazzaɓi (non-steroidal and ani-inflammatory drugs), kamar ibuprofen, diclofenac, naproɗen, indomethacin da sauran makamantansu, ya kan sa fitsari ya yi kumfa.

6. Cin abinci mai zaƙi sosai (sugar), ko ‘protein’ zalla ba tare da an sirka shi ba, shi ma ya kan sa fitsari ya yi kumfa sosai.

Fitsari Mai Kumfa Wanda Ke Da Matsala

Wannan na faruwa ne sakamakon:

1- Ciwon siga (diabetes): Idan mutum na da ciwon siga, Ƙodarsa na shan wahala wajen tacewa da kuma hana siga da ‘protein’ ɗin cikin jininsa daga shiga fitsarinsa. Da zarar sun shiga, fitsarinsa zai iya yin kumfa.

2- Ciwon Ƙoda (kidney disease): ko da mutum ba shi da ciwon siga, idan yana da ciwon Ƙoda, shi ma zai iya sa fitsarinsa ya yi kumfa.

3- Cutar mafitsara (urinary tract infection – UTI): Idan mutum yana da wannan cuta, ƙwayoyin cutar za su kasance a cikin fitsarinsa, don haka zai iya yin kumfa.

Fitsari
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post

Ƙarin Albashin Sojoji Ya Tunzura Ƙungiyar Ƙwadago Neman Ƙari

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.