Sabon tsarin albashin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi kwanan nan ga ma’aikatan rundunar soji, zai ɗaga albashin Janar na soja zuwa naira miliyan 3.25, yayin da na ƙananan sojoji zai koma naira 187,200.
Wannan ƙarin albashi, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumbar 2026, ya ƙunshi ƙarin da ya kama daga kashi 30 zuwa kashi 80 ga matsayi na soja daban-daban.
Ana sa ran sojoji kimanin 250,000 ne za su ci gajiyar wannan sabon tsarin albashi, wanda zai ƙara yawan kuɗin da ake kashewa, wajen biyan albashin sojojin a shekara daga naira biliyan 660 zuwa naira biliyan 924, kamar yadda wata sanarwa daga mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ta bayyana.
A ƙarƙashin sabon tsarin, jami’ai masu matsayi sama da na Kanal, za su samu ƙarin albashi na kashi 30. Wannan ya shafi Birgediya-janar, Manjo-janar, Laftanar-janar da kuma Janar.
Ma’aikata daga matsayin Kanal zuwa Waran ofisa, za su samu ƙarin kashi 50, yayin da waɗanda ke matsayin ‘Priɓate’ zuwa Sagen za su samu ƙarin kashi 80.
Ministan tsaro, Christopher Musa ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da tashar ‘News Central’ a watan da ya gabata cewa, gwamnatin Tinubu ta ƙara mafi ƙarancin albashin sojoji daga naira 49,000 zuwa naira 100,000.
Wani nazari da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa, naira 100,000 ɗin za ta iya ciyar da soja na tsawon kwana 21 ne kawai, bisa la’akari da rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), kan kuɗin abinci mai gina jiki (CoHD), wanda ya sanya kuɗin abinci mai gina jikin ko karin kumallo, ko abincin rana ko na dare ga mutum ɗaya a kan naira 1,589 a kowace rana.
Nazarin ya kuma nuna cewa, sojoji a wasu ƙasashen na Afirka, kamar Afirka ta Kudu, Nijar da Jamhuriyar Benin, suna samun albashin da ya zarce na takwarorinsu na Nijeriya da kashi 200 zuwa kashi 800.
Ƙungiyoyin farar hula, sun yi tambaya kan ko wannan albashin zai isa ya kula da soja da iyalinsa a cikin yanayin tattalin arziƙin da ake ciki a halin yanzu, inda farashin kayan masarufi ke ci gaba da hauhawa. Haka kuma, tsohon kakakin rundunar soji, Manjo Janar John Enenche (mai ritaya), ya yi kira da a ƙara albashin sojojin, inda ya ba da shawarar a sanya mafi ƙarancin albashin wata ya zama daga naira 250,000; hakan ya biyo bayan ganin cewa, albashin da ake biya a yanzu bai dace da yanayin tattalin arziƙin ƙasar ko kuma irin sadaukarwar da aikin soja ke buƙata ba.
Da yake yin tsokaci a kan batun ƙarin albashin, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa; matakin ƙara albashin sojojin na nufin karrama sadaukarwar da maza da matan rundunar ke yi, wajen tunkarar ƴan fashi, masu garkuwa da mutane, da ƴan ta’adda.
“Dole ne mu tallafa wa maza da matan da ke tabbatar da tsaronmu a gidajenmu tare da nuna godiya a kan ayyukan da suke yi wa ƙasarmu,” in ji Tinubu a cikin sanarwar.
Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko ga jin daɗin sojoji tare da inganta rundunar sojin ƙasa ta hanyar samar da sabbin makamai da kayan aikin zamani na fasaha.













