Yayin da Nijeriya ke tunkarar babban zaben shekarar 2027, wata karamar kungiyar mata, na neman samun gurbi a babban matakin siyasar kasar, inda suke da kwarewa a fannoni daban-daban da suka hada da; hada kan jama’a tun daga tushe, gudanar da harkokin jam’iyya, kiwon lafiyar jama’a, ayyukan jin kai, nishadantarwa da kuma kasuwanci.
Sai dai, duk da cewa; bayyanarsu na nuna yadda mata ke kara nuna sha’awar shiga babban matakin siyasa, sauya Anita Zugwai-Chukwu da jam’iyyar YPP ta yi, na nufin cewa; mata biyu ne kawai suka rage a takarar shugabancin kasa, bisa sabon yanayin da aka samu.
Matan da ke cikin wannan takara ta shekarar 2027, sun hada da Ada Elizabeth Fredrick Okwori ta jam’iyyar NDP, Esther Nkem Okereke ta jam’iyyar NRM, Hajja Bintu Konto ta jam’iyyar LP, da kuma Ofordile Peace Egobia ta jam’iyyar APP. Okwori da Okereke, suna takarar shugabancin kasa ne, yayin da Konto da Egobia ke takarar mataimakin shugaban kasa. An kuma zabi Ndidi Patience Key, a matsayin abokiyar takarar sabon dan takarar shugaban kasa, wanda ya maye gurbin Zugwai-Chukwu a jam’iyyar YPP.
A baya, Zugwai-Chukwu ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta zama ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar YPP, bayan an amince da ita ba tare da hamayya ba a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja, ranar 30 ga watan Mayun 2026. Sai dai, tun daga lokacin jam’iyyar ta maye gurbinta da Peter Agada a matsayin dan takararta na shugabancin kasa.
Wannan lamari ya kara bayyana yadda wakilcin mata a babban matakin siyasar Nijeriya ke cikin yanayi mara tabbas ko rashin karfi.
Matan Da Ke Neman Jagoranci
Ada Okwori, shugabar jam’iyyar NDP ta kasa, ta zama ‘yar takarar shugaban kasa ta jam’iyyar, bayan an cimma matsaya ta hanyar tattaunawa tsakanin sassan jam’iyyar a fadin kasar.
Okwori, ‘yar kabilar Idoma ce daga Jihar Benuwe, kuma ‘yar asalin Otukpo; ta dade tana harkokin siyasa ta hanyar jam’iyyar PDP da kuma ayyukan hada kan jama’a tun daga matakin mazabu. Ita ce ta kafa shirin “Ward2Ward,” wanda ke karfafa gwiwar jama’a wajen shiga harkokin siyasa a matakin unguwanni.
Manufofinta na siyasa sun ta’allaka ne a kan shiga cikin al’umma, hada mata da matasa, jin dadin jama’a da kuma habaka ababen more rayuwa. Ta kuma yi magana game da tasirin siyasar kudi da ubangida a siyasa.
Kalubalen da take fuskanta a halin yanzu su ne, yadda za ta mayar da wannan asalin al’umma zuwa ganuwa da kuma samar da tsari mai kyau a dukkanin fadin kasar a fagen shugabancin kasa mai cike da kalubale.
Esther Nkem Okereke tana iya zama mafi shahara a tsakanin ‘yan takarar shugabancin kasar.
Jarumar ‘yar wasan kwaikwayo ta Nollywood, kuma furodusa a fina-finai, ta kuma yi aiki a fannin kasuwanci, agaji da saka hannun jari. Ta fito a matsayin ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar NRM, a babban taron jam’iyyar da aka yi a Abuja, ranar 29 ga Mayun 2026, bayan ta fafata da sauran masu neman takarar.
Ajandar ESTHER ta fi mayar da hankali ne kan ilimi, tsaro, kimiyya da fasaha, gidaje da kuma kasuwanci. Ta gano rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, cin hanci da rashawa da raunin hukumomi a matsayin wasu manyan kalubalen kasar.
A kan tikitin mataimakin shugaban kasa, akwai mata kwararru, gogaggu, kusan masu akida da manufofi iri daya.
Hajja Bintu Konto, mataimakiyar dan takarar jam’iyyar Labour Party, Dakta Chibuzo Sunday Okereke, kwararriya ce a fannin kiwon lafiya da jin kai, wacce ke da gogewa sama da shekaru talatin a fannin kiwon lafiya, ci gaban al’umma da kuma ayyukan agaji.
Ta yi aiki da Catholic Relief Serbices, ciki har da ayyuka a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, inda ta shiga shirye-shiryen yi wa al’ummomi masu rauni hidima da kuma wadanda suka rasa matsugunai.
Ayyukanta na sana’a, sun hada da lafiyar jama’a, abinci mai gina jiki, ruwa, tsafta, jin kai da kuma ci gaban al’umma. Tana da digiri na biyu a fannin lafiyar jama’a, kuma tana da gogewa a fannin ilimin lafiyar al’umma.
Ofordile Peace Egobia, ita ce ‘yar takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APP, kuma abokiyar takarar Kabiru Yusuf. Idan aka kwatanta ta da sauran mata, bayanan da ake samu game da iliminta na sana’a da siyasa suna da matukar yawa.
Patience Ndidi Key (PNK), mataimakiyar Peter Agada ta YPP, kwararriyar ma’aikaciyar kiwon lafiya ce, ‘yar Nijeriya da ke zaune a Amurka, ‘yar kasuwa kuma ‘yar siyasa. Ta maye gurbin Anita Zugwai-Chukwu, wacce aka fara nada ta a matsayin abokiyar takarar Agada.
Key ita ce jagora, kuma Shugabar Kungiyar ‘Yan Kasuwa ta ‘Yan Nijeriya da ke Kasashen Waje (NiDCC), kuma tana da himma a harkokin siyasar Nijeriya. Ta taba tsayawa neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PRP, kafin zaben 2023.
Har ila yau, kasancewar mata a jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa, abu ne mai matukar muhimmanci. Sai dai, idan aka kwatanta shi da tarihin siyasar Nijeriya, yana kuma nuni da yadda aka dan samu sauye-sauye.
Kafin sauyin da jam’iyyar YPP ta yi, mata uku ne cikin ‘yan takarar shugaban kasa 19 da aka bayyana, don zaben 2027, wanda ya kai kusan kashi 16 cikin dari na jimillar ‘yan takarar. Bayan maye gurbin da aka yi da Zugwai-Chukwu, mata biyu ne kawai suka rage a cikin jerin ‘yan takarar shugaban kasar a halin yanzu.














