ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

by Sulaiman
6 hours ago

Mahawaranmu ta wannan makon, ta kasance ne a kan jin ra’ayoyin, dangane da dawo da tallafin man fetur ko barin sa. Wannan cece-kuce, shi ne kusan abin da ya fi ɗaukar hankalin ƴan Nijeriya a yanzu, tun bayan da ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya bayyana dawo da shi bayan lashe zaɓen 2027. Kamar kowane mako, SANI ANWAR da MUHAMMAD BAƘIR ne ke tattaro ra’ayoyin naku.

Aminu Danladi
Gaskiya ba na goyon bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi. Dalili kuwa, abin yana komawa ne kan talaka, a daidai lokacin ne komai yake ƙara tashi, kama tun daga kan harkokin sufuri da kayan abinci da sauran kayan masarufi.

Sani Abdullahi Shansharai
Ko kaɗan, ba na goyon bayan sake dawowa da tallafin man fetur, dalili kuwa, ko da an sake dawowa da shi, idan wata gwamnatin ta zo sai ta sake cirewa, wanda hakan zai iya zama kwan-gaba-kwan-baya.

ADVERTISEMENT

Shawarata da gwamnati kaɗai ita ce, wajibi ne ta sa ido ta kuma yi abin da ya kamata, musamman ta fuskar aiwatar da tsare-tsaren da su taimaki talaka. Misali, kamar samar da sauƙi ta fuskar harkokin sufuri, gyaran matatun man fetur da muke da su da sauran makamantansu.
Har ila yau, wajibi ne gwamnatin tarayya ta jajircewa wajen ganin gwamnoni sun yi amfani da maƙudan kuɗaɗen da suke samu, wajen hidimta wa talakawansu.

Sannan, idan muka duba, tun da aka cire wannan tallafi aka yi sallama da matsalar ƙarancin man fetur a wannan ƙasa, iya kuɗinka, iya shagalinka.

LABARAI MASU NASABA

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

Adam Isa Waziri
A ganina, tallafin man fetur ya fi amfani ga ɗan ƙasa fiye da cire shi. Saboda, idan farashin fetur yana da sauƙi, ba wanda yake da mota kaɗai yake samun sauƙi ko amfana ba. Talaka ma yana amfana ta hanyar rage kuɗin sufuri, sannan hakan yana taimakawa, wajen rage tsadar abinci da sauran kayan masarufi.

Ko mutum ba shi da mota, yana amfani da sufuri, kuma motocin da ke ɗaukar kayan abinci da sauran kayayyaki, suna amfani da fetur. Saboda haka, idan fetur ya yi tsada, kusan kowa yana jin tasirin a jikinsa.

Amma idan aka cire tallafin, farashin fetur ya tashi, sufuri ya tashi, kayan abinci suka ƙara tsada, kuma rayuwa ta ƙara wahala. Shi ya sa a ganina, ko da akwai matsaloli a tsarin tallafin, aƙalla ɗan ƙasa yana samun amfaninsa a zahiri. Don haka, ni ina ganin tallafin man fetur ya fi zama alheri ga ɗan ƙasa fiye da cire shi.

Yusuf Usama Muhammad
Mu matasa ba mu da matsala da sauyi, matsalarmu ita ce; rashin tsari. Cire tallafin ba tare da an kawo wani tsari mai kyau ba, shi ke lalata ƙasa. Yanzu ɗalibi yana biyan kusan naira 50,000 a kan sufuri a kowane wata, kuɗin karatu a jami’a ya tashi, kuma babu aiki bayan kammala karatu.

Saboda haka, muna cewa, kada ku dawo da tallafin mai, madadin haka, ku bincika kowane gidan mai ƙaramin ƙarfi, ku ba shi 50,000 a kowane wata. Ku rage kuɗin karatu a jami’a da kasha 50 cikin 100. Sannan ku samar da ayyukan yi na gwamnati ga matasa. Ku saka kuɗin a noma da fasaha, ya zama an inganta rayuwanmu, hakan shi ne ya fi.

Muhammad Sani, Abuja
Yawancin mutane suna magana a kan dawo da tallafin mai kamar hakan shi zai sauƙaƙa rayuwa. Amma ainihin matsalar ba ita ce kawai ba. Idan gwamnati ta mayar da tallafin mai, za ta ce “muna biyan tallafi. Don haka, ba mu da isasshen kuɗi.” A wannan hali, za su iya rage albashin ƙaramin ma’aikaci daga naira 70,000 zuwa ƙasa, ko kuma su ƙi ƙara shi.

Har ila yau, da yawa daga cikin ma’aikatan da ke karɓar ƙaramin albashi, za su fara jira albashinsu. Gwamnati za ta yi amfani da hujjar cewa, “kuɗin tallafin mai ya cinye kuɗin da za a biya albashi da shi.” Wannan ya faru a baya, kuma yana iya faruwa a nan gaba.

Saboda haka, ba za a iya samun tallafin mai da albashin naira 70,000 a lokaci guda ba, dole ne daƙile ɗaya daga cikinsu. Idan an mayar da tallafi, ƙarfin sayayya na ma’aikaci zai iya ƙaruwa a ɗan lokaci, amma albashin kansa zai iya kasawa. Wannan shi ne ainihin matsalar da ya kamata a yi magana a kai, ba kawai a dawo da tallafi ba.

Ahmad Bello
Ni dai a raayina, na fi son a dawo da tallafin mai. Saboda lokacin da gwamnati ke biyan tallafi, komai yana nan a farashi wanda kowa ke iya saya. Amman lokacin da aka cire tallafin, abubuwa sun yi tsadar gaske matuƙa. Don haka, muke tunani idan aka dawo da shi abubuwa za su yi sauƙi, kuma mutane za su samu damar saya ba tare da wani tashin hankali ba.

Muhammad Nasir Mukhtar
Janye tallafin man fetur, tamkar buɗe ƙofar azaba ce mafi muni ga talakawan Nijeriya a tarihin ƙasar.

Cire tallafin man fetur da gwamnatin Nijeriya ta yi a shekarar 2023, ya bayyana ne a matsayin wani mataki na rage nauyin da tallafin ke yi wa baitulmalin gwamnati a cewar gwamnatin ƙasar. Sai dai, akwai hujjojin da ke nuna cewa; hanyar da aka bi domin aiwatar da wannan hukunci ya jefa dubban talakawan Nijeriya cikin mawuyacin hali.

A cewar Bankin Duniya, farashin fetur ya ƙaru da matsakaicin kaso kusan 163 cikin 100, bayan cire tallafin da sauran sauye-sauyen tattalin arziƙi. Wannan ya shafi sufuri, farashin abinci, noma da ƙananan sana’o’i, musamman ganin yadda gidaje da ƴan kasuwa da dama ke dogaro da fetur wajen samar da wutar lantarki tare da gudanar da al’amarunsu na yau da kullum.
Bankin Duniya, ya kuma ƙiyasta cewa; cire tallafin ya bai wa gwamnati damar tanadin kuɗi kusan naira tiriliyan biyu a 2023, sannan kuɗaɗen sun haura naira tiriliyan 11 zuwa ƙarshen 2025.

Amma babban abin tambaya a nan shi ne, ta yaya waɗannan kuɗaɗen suka koma cikin rayuwar talakawa, domin talakawa na iya cewa; ba su gan a ƙasa ba.

Bankin Duniya, ya yi gargaɗin cewa; idan ba a samar da isasshen tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi ba, ƙarin farashin fetur zai iya ƙara talauci tare da tilasta wasu iyalai rage kashe kuɗaɗen ilimi da lafiya.

Rahoton Reuters na Agustan 2026 kuma ya nuna cewa, matsalar tsadar rayuwa na ci gaba da addabar ƴan Nijeriya, yayin da farashin fetur ya kai kusan sau shida na abin da yake kafin cire tallafin.

Saboda haka, sukar cire tallafin ba lallai ya kasance kira ne na komawa tsohon tsarin ba. Muhimmin abin da ake buƙata shi ne, a tabbatar da cewa; kuɗaɗen da aka tanada daga wannan sauyi sun koma wajen rage raɗaɗin rayuwa, inganta ayyukan jama’a da tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi.

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara
  • Sulaiman
    Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa
  • Sulaiman
    Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

MASU ALAKA

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku
Labarai

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro
Labarai

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18
Labarai

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Next Post
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam'iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

LABARAI MASU NASABA

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.