A wata hira da ya yi da gidan talabijin na channels ministan tsaron Nijeriya Christopher Musa ya yi game da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i na cigaba da tada kura a kafafen sadarwa na zamani da kuma manyan jaridun ƙasar.
Kalaman na sa na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan yake tsare kimanin watanni biyar a hannun hukumar ICPC bisa wasu tuhume-tuhume da suke da alaƙa da cin hanci da rashawaMinistan dai ya yi wasu kalamai da ake ganin wata manuniya ce da ke nuna goyon bayan a cigaba da riƙe tsohon gwamnan jihar Kaduna duk da irin kiraye-kirayen da ake yi na a sake shi.
Daga cikin zarge-zargen da ministan tsaron ya yi harda cewa lokacin mulkin Malam Nasiru El-Rufa’i ɗan kudancin Kaduna bayan iya zuwa arewacin ta ya nuna kansa zai fuskanci matsala.
Christopher Musa dai ya amsa tambayar da aka yi masa ta yadda zai iya yi cin zaɓen rumfar sa, inda shi kuma ya ce yanzu haka yana koyan siyasa a wajen adalin gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani wanda ya ce tun a shekarar ta farko ya nuna haka.
Ya ƙara da cewa Malam Nasiru El-Rufa’i ya raba jihar Kaduna gida biyu inda ɗan kudancin Kaduna bai isa ya je arewacin ta ya nuna kan sa ba, haka shim ɗan arewacin Kaduna bai isa ya je kudancin ta baSai dai a cewar Christopher Musa yanzu gwamnan jihar Kaduna Uba Sani a shekarar guda ya daidaita komi babu wannan bambanci da ya bayyana da farko a tsakanin ɗan kudancin Kaduna da kuma na arewacin ta”
Ba Mu taɓa yin murnar da mulkin Malam Nasiru El-Rufa’i ba, mutumin da baya da aiki sai yadda za a kashe mutane a jihar Kaduna me zai sa mu yi murna da mulkin sa’ zargin Christopher MusaMinistan tsaron ya ce cikin izza da ɗagawa tsohon gwamnan ke bayyana irin yadda ya zalunci mutanen jihar Kaduna ya ce irin jama’ar da aka kashe a yankin Kaduna ta kudu ba za a iya haɗawa da yanzu ba.Wannan batu dai yana cigaba da ya mutsa hazo ta inda jama’a ke yi wa abin fassara daban-daban tare da alaƙanta maganganun na ministan tsaron baki ɗayansu da siyasa.
Daga cikin masu yi wa ministan tsaron raddi sun riƙa jefa tambayoyi akan cewa ya tuna da tarihin jihar Kaduna ta jima tana fama da rikice-rikicen addini da na ƙabilanci tare da faɗin cewa ina Christopher Musa yake a wannan lokacin?
Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum sun ja hankalin ministan tsaron da cewa ya kamata gwamnati da jami’anta su riƙa taka-tsantsan wajen furta kalamai, ko a lokacin zaman lafiya ko lokacin rikici.
A cewar su kalamai irin waɗannan da ake kallon su na siyasa zalla da jami’an gwamnati ke yi na iya ƙara ta’azara rashin yarda da juna, tare da sanya shakku ga ƴan ƙasa su yarda cewa gwamnati bana tafiyar da al’amura cikin adalci a wannan yanayi na siyasa.Haka kuma a bangare guda akwai masu kallon waɗannan kalamai na ministan tsaro a matsayin tsantsan son kai ne, ko nuna ɓangaranci, wanda hakan zai iya raunana amincewar mutane akan sa.Idan za a iya tunawa daga abubuwan da tsohon gwamnan ya riƙa ayyana wa a matsayin batutuwa da zai maida hankali akan su idan ya samu nasarar zama gwamnan jihar Kaduna su ne yaki da ƴan ta’adda da kuma kawo ƙarshen faɗace-faɗacen da jihar ke fama da su a wancan lokacin.
Duk da cewa jama’a da dama suna da bambancin ra’ayi na siyasa da wasu abubuwa da Malam Nasiru El-Rufa’i bai hana su bayyana ra’ayin su akan waɗannan kalamai na ministan tsaro ba inda da yawa ke ganin rashin dacewar tare da hangin ana iya maida hannun agogo baya.
Mutane irin su Malam Lawal Mai Fetur Unguwar Rimi suna da ra’ayin cewa Christopher Musa ya cire kakin soja ya sanya rigar siyasa ya zama “Data Boys” na shugaba Tinubu, wanna ba zai hana idan ya yi magana ba daidai ba su yi masa martani.
Malam Lawal mai fetur ya ƙara da cewa kalaman na ministan tsaro kalaman tada hankali ne, inda ya ce jihar Kaduna na cin gajiyar zaman lafiya da Malam Nasiru El-Rufa’i ya samar a yankin kudancin Kaduna neYa ƙara da cewa kalaman na ministan tsaro butulci ne tsan-tsan saboda Malam Nasiru El-Rufa’i ya tsaya kai da fata wajen ganin Bola Ahmad Tunibu ya samu nasarar lashe zaɓen 2023 amma gashi da irin abubuwan da zai saka masa da su ke nanYa ce hatta tsohon miƙamin da ya riƙe na shugaban rundunar sojojin Nijeriya Malam Nasiru El-Rufa’i ne ya tsaya masa har ya kai ga samun shi, amma Christopher Musa bai amfanar da jihar Kaduna da komi ba har ya sauƙa daga muƙamin.
Sai dai tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya fito ya kare ministan tsaron, yana mai cewa ba za a iya yin watsi da abubuwan da wasu mazauna kudancin Kaduna suka ce sun fuskanta a lokacin mulkin El-Rufa’i ba.
Babachir Lawal ya ce masu goyon bayan tsohon gwamnan suna da ƴancin kare shi, amma hakan bai kamata ya shafe koke-koken da wasu daga cikin al’ummar kudancin Kaduna suka daɗe suna bayyanawa ba.
A cikin wani kwatance mai matuƙar tayar da kura, Lawal ya ce yadda wasu daga kudancin Kaduna ke kallon El-Rufa’i ya yi kama da yadda Yahudawa ke kallon Adolf Hitler.
Ya kuma ce gwamnatin Gwamna Uba Sani tana ƙoƙarin warkar da tsofaffin raunukan da rikice-rikicen siyasa da na al’umma suka haifar a jihar Kaduna a lokacin mulkin Malam Nasiru El-Rufa’i
Sai dai duk wannan da toka-sa-katsi da ake yi bai hana iyalan tsohon gwamnan bayyana na su ra’ayin ba, inda suka nemi da ministan tsaron Nijeriya Christopher Musa da ya janye waɗannan kalamai na shi akan mahaifin su.
Iyalan dai sun bai wa Ministan tsaron wa’adin kwanaki 7 ko dai ya tabbatar da maganganun sa tare da bada shaida a bainar jama’a ko kuma ya bada hakuri akan wannan iƙirarin da ya yi na cewa tsohon gwamnan ya shirya kashe mutenen yankin kudancin KadunaMartanin dai ya biyo bayan wancan zargi inda ɗaya daga cikin ƴa ƴan tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i wato Mohammed Bello El-Rufa’i ya fitar da sanarwa a madadin iyalan inda ya nemi Christopher Musa da ya janye kalaman sa.
A cewar iyalan za su za su bi duk hanyoyin shari’a idan ministan ya gaza janye furucin da ya yi ko kuma ya kasa gabatar da hujjojin da ke tabbatar da abin da ya faɗa.














