Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce shirin da yake da shi na dawo da tallafin man fetur ba zai kasance tallafin man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje ba, sai dai tallafin samar da man a cikin gida. Ya ce manufar ita ce rage farashin fetur da kuma kuɗin sufuri.
Atiku ya bayyana cewa gwamnati za ta tallafa wa matatun mai na cikin gida domin su samu damar tace ɗanyen mai cikin rahusa, sannan a rage farashin da ake sayar da fetur ga masu amfani da shi. Ya kwatanta tsarin da tallafa wa masu yin takalma a Aba maimakon kashe kuɗin gwamnati wajen rage farashin takalman da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
A cewarsa, manufar ba wai rage farashin fetur kaɗai ba ce, har da rage tsadar rayuwa ta hanyar rage kuɗin sufuri, jigilar kayan abinci daga gonaki zuwa kasuwanni da kuma kuɗin makamashin da ’yan kasuwa ke kashewa.
Atiku ya ce idan aka rage kuɗin fetur da sufuri, hakan zai taimaka wajen rage farashin kayan abinci da sauran buƙatun yau da kullum, tare da ƙara kuɗin da ke saura a hannun ’yan Nijeriya.
Ya ce manufarsa ita ce a sake samun sauƙin rayuwa a Nijeriya, yana mai cewa shirin tallafin samar da man a cikin gida zai taimaka wajen ƙarfafa matatun cikin gida, samar da ayyukan yi da kuma rage farashin fetur.














