Gwamnatin Tarayya ta ce tana aiki don rage hauhawar farashi kayayyaki zuwa ƙasa da kashi 10 cikin 100, in ji mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga.
Onanuga ya ce gwamnati na ɗaukar wasu matakai domin taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen rage tashin farashin man fetur sakamakon rikicin a duniya.
Ya ce Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC) zai sayar da man fetur a farashin da ya saya na tsawon kwanaki 30, ta hanyar haƙura d ribar da yake samu.
Matakin na da nufin rage tasirin tsadar man fetur, musamman ga masu motocin haya da sauran ‘yan Nijeriya masu fama da matsin tattalin arziƙi.
Onanuga ya jaddada cewa matakin ba wai na nufin gwamnati ta dawo da tallafin man fetur ba ne.
Ya kuma ce gwamnati na shirin ɗaukar wasu manyan matakan tattalin arziƙi domin rage hauhawar farashi zuwa kasa da kashi 10 cikin 100 nan gaba kaɗan.














