Mutane uku sun ƙone kurmus bayan wata bas mai ɗauke da kajin da aka ƙyanƙyashe ‘yan kwana ɗaya ta yi karo da wata babbar mota a yankin Oko-Olowo da ke Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Hatsarin ya faru ne cikin tsakar daren ranar Alhamis, lokacin da babbar motar da ta taso daga Shao ke ƙoƙarin yin juyawa zuwa Oko-Olowo, sai motar bas ɗin da ta taso daga Legas ta buge ta.
Karfin karon ya haddasa gobara wadda ta ƙone bas ɗin, inda dukkanin mutane uku da ke cikinta suka ƙone har lahira.
Wani ganau ya ce jami’an Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) sun isa wurin da sanyin safiyar Juma’a domin kwashe gawarwakin waɗanda suka rasu.
Kwamandan FRSC na Jihar Kwara, Kabiru Kazeem, ya tabbatar da faruwar hatsarin, amma bai yi ƙarin bayani ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.














