ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NDLEA Ta Cafke Kwayoyin Tramadol Miliyan 1.63 Da Akai Nufin Shigar Da Su Kano

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama ƙwayoyin tramadol miliyan 1.63 da aka ɓoye a cikin manyan motocin dakon kaya guda biyu da ke kan hanyarsu daga Legas zuwa Kano. Hukumar ta ce kamen wani ɓangare ne na sumamen da take yi kan wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke aiki tsakanin ƙasashe.

A cewar NDLEA, jami’anta sun fara tare wata motar a ranar 2 ga Yuli a kan titin Lagos-Ibadan, inda suka gano ƙwayoyi 853,000 na tramadol mai ƙarfi 250mg da aka ɓoye a wani sashi da aka ƙera ƙarƙashin motar. An kama direban motar mai suna Jabir Kabiru, mai shekaru 22. Bayan kwana biyu kuma, aka sake kama wata motar a hanya ɗaya da ke ɗauke da kwayoyi 777,000, tare da cafke direbanta Muhammed Nuhu, mai shekaru 22.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta kama wasu ƙwallaye biyu na tabar wiwi ta zamani (Canadian Loud) masu nauyin kilo 4.7 a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja. An ce an shigo da kayan ne daga Kanada ta jiragen British Airways da Ethiopian Airlines. Bincike ya kai ga kama wasu mutane huɗu, ciki har da wata ‘yar kasuwa mai suna Chioma Nneka Mokeme, wadda ta amsa cewa wani abokinta da ke Kanada ne ya shigar da ita harkar safarar miyagun ƙwayoyi.

ADVERTISEMENT

A wasu sumame daban, NDLEA ta kama wani tsoho mai shekaru 80, Chika Ugwoji, a Jihar Ribas tare da gram 800 na tabar wiwi. A Jihar Edo kuma, an kama ma’aurata da ake zargi da adana miyagun ƙwayoyi, inda aka ƙwace buhuna 22 na tabar wiwi da kuma Canadian Loud masu nauyin sama da kilo 400 gaba ɗaya.

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yabawa jami’an hukumar bisa nasarorin da suka samu, tare da ƙarfafa su su ci gaba da yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Abubakar Sulaiman
    Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa

MASU ALAKA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Asibitin Burkina Faso

Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Asibitin Burkina Faso

LABARAI MASU NASABA

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.