Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen Jihar Edo ta kama wani dattijo mai shekaru 58, Musa Muhammed, da wasu mutane takwas bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.
Kwamandan NDLEA na Jihar Edo, Mitchel Ofoyeju, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Benin, inda ya ce waɗanda aka kama sun ƙunshi maza biyar da mata huɗu, waɗanda ake zargin an same su da nau’o’in miyagun ƙwayoyi daban-daban.
A cewarsa, an kama mutanen tara ne yayin wasu samame da jami’an hukumar suka gudanar a wurare daban-daban da ake zargin cibiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi ne a faɗin jihar.
Kwamandan ya bayyana sunayen sauran waɗanda aka kama da Ebere Anthony, mai shekaru 55; Gift Oliseyenum, 31; Boniface George, 27; Muzamilu Mustapha; Faustina Peter, 27; Chucks Odili, 36; Anna Agbona, 17; da Julius Enebuli, 42.














