Rundunar sojin Nijeriya ta ce ba za ta tsagaita wuta da ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ba, inda ta bayyana cewa za ta ci gaba da kai wa ƙungiyoyin hare-hare.
Mai magana da yawun rundunar sojin, Manjo-Janar Samaila Uba ne, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron bayanan sirri da aka gudanar a Abuja.
Ya ce hare-haren soji na baya-bayan nan sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama, kama wasu tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Uba ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da matsa wa ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai lamba duk da ƙaruwar hare-hare a sansanonin soji a Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Ya kuma bayyana cewa Nijeriya na tattaunawa da ƙasashen yankin Sahel da suka fice daga ECOWAS domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro.













