ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 7, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayayya Ta Kwace Kwalbar Lemo 5,964 A Kano

by Abubakar Sulaiman
12 hours ago
Kasuwar

Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Jihar Kano (KCPC) ta kwace kwalaben lemun kwalba da suka kai 5,964 waɗanda wa’adin amfaninsu ya ƙare a Kasuwar Singer da ke jihar Kano. Hukumar ta ce ana zargin wani ɗan kasuwa ya tanadi kayayyakin ne domin sayar wa jama’a ba tare da sanin cewa sun ƙare ba.

Daraktan Ayyukan Bincike da Kwace Kayayyakin da Ba Su Inganta Ba na hukumar, Alhaji Auwalu A. Muhammad, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a, Jamilu Mustapha, ya fitar ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026.

A cewarsa, hukumar ta samu ƙorafi kan wani ɗan kasuwa da ake zargin ya tanadi lemun kwalba masu yawa waɗanda wa’adin amfaninsu ya ƙare. Bayan samun bayanin, jami’an hukumar sun garzaya kasuwar domin gudanar da bincike da kwace kayayyakin kafin su shiga hannun masu sayayya.

ADVERTISEMENT
Kasuwar

Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike a kasuwanni, da shaguna da manyan kantuna domin gano wa tare da cire kayayyakin da wa’adinsa suka ƙare, ko suka lalace ko ba su cika ƙa’idojin inganci ba. Ta kuma gargaɗi ’yan kasuwa da kada su ɓoye kayayyakin da wa’adinsa suka ƙare ko su yi ƙoƙarin sauya bayanan wa’adin amfani da ke jikin marufinsu.

Babban Sakataren hukumar, Dr. Ibrahim Garba-Muhammad, ya yi kira ga ’yan kasuwa da su riƙa duba kayayyakinsu akai-akai tare da cire waɗanda suka ƙare daga shaguna. Ya kuma gargaɗi duk wanda zai yi ƙoƙarin tsoratar da jami’an hukumar, yana mai cewa suna gudanar da ayyukansu ne bisa doka domin kare lafiyar al’umma.

LABARAI MASU NASABA

Shari’ar Zargin Juyin Mulki: Me Ya Shigar Da Bidiyon Binciken Sojoji Kotu?

Ƙarancin Ruwa Da Iskar Gas Ne Sanadin Raguwar Samun Wutar Lantarki A Nijeriya

Kasuwar
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    NDLEA Da FRSC Za Su Ƙaddamar Da Gwajin Ƙwayoyi Na Dole Ga Direbobin Motocin Haya
  • Abubakar Sulaiman
    Tallafin Naira 70,000 Ya Nuna Tinubu Na Ƙaunar Ma’aikata – Oshiomhole
  • Abubakar Sulaiman
    Kotu Ta Gurfanar Da Mutane Biyu Kan Zargin Kashe Wani Matashi Saboda Kare A Kano
  • Abubakar Sulaiman
    ADC Za Ta Ɗaukaka Ƙara, Shugabancin David Mark Da Aregbesola Ne Kawai Ta Amince Da Shi

MASU ALAKA

Juyin Mulki: Kotu Ta Yi Watsi Da Iƙirarin Azabtar Da Waɗanda Ake Zargi, Ta Amince Da Bayanan Da Suka Bayar
Labarai

Shari’ar Zargin Juyin Mulki: Me Ya Shigar Da Bidiyon Binciken Sojoji Kotu?

November 6, 2026
Matsanancin Rashin Lantarki Ya Addabi ‘Yan Nijeriya
Labarai

Ƙarancin Ruwa Da Iskar Gas Ne Sanadin Raguwar Samun Wutar Lantarki A Nijeriya

November 6, 2026
Juyin Mulki: Kotu Ta Yi Watsi Da Iƙirarin Azabtar Da Waɗanda Ake Zargi, Ta Amince Da Bayanan Da Suka Bayar
Manyan Labarai

Juyin Mulki: Kotu Ta Yi Watsi Da Iƙirarin Azabtar Da Waɗanda Ake Zargi, Ta Amince Da Bayanan Da Suka Bayar

November 6, 2026
Next Post
Tallafin Naira 70,000 Ya Nuna Tinubu Na Ƙaunar Ma’aikata – Oshiomhole

Tallafin Naira 70,000 Ya Nuna Tinubu Na Ƙaunar Ma’aikata - Oshiomhole

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Kasance Abokiya Ga Kasashen Afirka Da Suka Fi Amincewa Da Dogaro Da Ita

Sin Ta Kasance Abokiya Ga Kasashen Afirka Da Suka Fi Amincewa Da Dogaro Da Ita

November 6, 2026
Daga Rumfar Baje Koli Zuwa“China Haul”—Bari Mu Leka Dalilin Da Ya Sa Sin Ke Iya Samar Da Ingantattun Kayayyaki Masu Araha A Duniya

Daga Rumfar Baje Koli Zuwa“China Haul”—Bari Mu Leka Dalilin Da Ya Sa Sin Ke Iya Samar Da Ingantattun Kayayyaki Masu Araha A Duniya

November 6, 2026
Xi Jinping Ya Gana Da Twakaransa Na Gabon

Xi Jinping Ya Gana Da Twakaransa Na Gabon

November 6, 2026
Juyin Mulki: Kotu Ta Yi Watsi Da Iƙirarin Azabtar Da Waɗanda Ake Zargi, Ta Amince Da Bayanan Da Suka Bayar

Shari’ar Zargin Juyin Mulki: Me Ya Shigar Da Bidiyon Binciken Sojoji Kotu?

November 6, 2026
Shawarwarin Sin Na Ci Gaba Da Ingiza Sabon Kuzari Wajen Rayawa Da Jagorantar Harkokin Intanet A Duniya

Shawarwarin Sin Na Ci Gaba Da Ingiza Sabon Kuzari Wajen Rayawa Da Jagorantar Harkokin Intanet A Duniya

November 6, 2026
Makon Teku Na Duniya Na 2026 Ya Haskaka Rawar Da Sin Ke Takawa A Fannin Jagorancin Teku

Makon Teku Na Duniya Na 2026 Ya Haskaka Rawar Da Sin Ke Takawa A Fannin Jagorancin Teku

November 6, 2026
Matsanancin Rashin Lantarki Ya Addabi ‘Yan Nijeriya

Ƙarancin Ruwa Da Iskar Gas Ne Sanadin Raguwar Samun Wutar Lantarki A Nijeriya

November 6, 2026
An Fitar Da “Shawarar Kafa Sabon Matakin Dakile Da Kandagarkin Cututtuka Masu Yaduwa Tsakanin Sin Da Afirka”

An Fitar Da “Shawarar Kafa Sabon Matakin Dakile Da Kandagarkin Cututtuka Masu Yaduwa Tsakanin Sin Da Afirka”

November 6, 2026
Juyin Mulki: Kotu Ta Yi Watsi Da Iƙirarin Azabtar Da Waɗanda Ake Zargi, Ta Amince Da Bayanan Da Suka Bayar

Juyin Mulki: Kotu Ta Yi Watsi Da Iƙirarin Azabtar Da Waɗanda Ake Zargi, Ta Amince Da Bayanan Da Suka Bayar

November 6, 2026
Kasar Sin Na Fadada Ci Gaban Fasahar Amfani Da Motoci Masu Lantarki Ga Kasashen Afrika

Kasar Sin Na Fadada Ci Gaban Fasahar Amfani Da Motoci Masu Lantarki Ga Kasashen Afrika

November 6, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.