Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe wata matar aure mai shekaru 35, Fatima Abubakar, da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke Kano, a ranar 17 ga watan Janairu, 2026.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin, Umar Auwalu mai shekaru 23 da Yakubu Daiyebu mai shekaru 21, an yi musu hukuncin ɗaurin rai da rai bisa laifukan haɗa baki wajen kisan kai da fashi da makami.
Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Nasiru Saminu ya bayyana kisan a matsayin ɗaya daga cikin munanan laifuka da suka girgiza tarihin shari’a a jihar.
Alƙalin ya ce waɗanda aka kashe sun rasa rayukansu ne a hannun mutanen da suka aminta da su.
Ya ƙara da cewa Fatima ce ta buɗe wa Umar ƙofa lokacin da ya zo tare da abokin aikata laifinsa, ba tare da sanin cewa suna da niyyar kashe su ba.
Mai shari’a Saminu ya jajanta wa iyalan mamatan, musamman Haruna Bashir, mijin Fatima kuma mahaifin yaran shida.
Ya ce babu wani hukuncin kotu da zai iya dawo da rayukan mamatan ko kuma ya biya iyalan diyya da ta dace da irin wannan rashi.
Kotun ta same su da laifin kisan kai da hukuncinsa ya kai ga kisa, bisa sashe na 221 na kundin dokokin Penal Code.
Sai dai kotun ta sallami mutum na uku mai suna Isyaku Yakubu, mai shekaru 40, tare da wanke shi daga dukkanin zarge-zargen da ake masa.













