Dakarun rundunar Operation FANSAN YAMMA sun kama wani da ake zargi da ta’addanci mai suna Auta Maikyala a wani asibiti da ke ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
An kama wanda ake zargin ne a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2026, lokacin da ya je neman magani sakamakon raunin harbin bindiga da ya samu a wani artabu da wata ƙungiyar masu aikata laifi.
Rundunar sojin ta ce bincike ya nuna cewa ana zargin mutumin da hannu a hare-hare, garkuwa da mutane da satar shanu.
A halin yanzu, yana hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike.
A wani samame na daban, sojoji sun kakkabe maɓoyar ‘yan ta’adda a ƙauyuka uku da ke ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Haka kuma, rundunar sojin saman Nijeriya ta kai hare-haren sama kan wasu wuraren da ake zargin ‘yan ta’adda masu alaƙa da ƙasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Dogo Gide, suke amfani da su a Babban Doka da dajin Kuyumbana.
Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ta kuma buƙaci jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan ayyukan masu aikata laifuka.













