Masu amfani da layin MTN da aka zaɓa domin amfana da tallafin Naira 50,000 na wata-wata da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa za su iya duba cancantarsu ta hanyar latsa *671*0#.
Shirin mai suna National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI) an ƙirƙiro shi ne domin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a Nijeriya.
Kamfanin MTN ya gargaɗi masu amfani da layinsa kan saƙonnin bogi da ake tura musu tare da neman su danna kalmar “YES” zuwa wasu lambobi domin samun tallafin.
Kamfanin ya ce saƙonnin ba gaskiya ba ne, tare da jan hankalin jama’a da ka da su bayyana lambobin sirrinsu, ko lambobin OTP.
Waɗanda aka zaɓa za su samu saƙon kar ta kwana daga kamfanonin da ke kula da biyan kuɗin, domin neman amincewarsu kafin a tura musu kuɗin.
Masu amfani da MTN da suka cancanta za su karɓi tallafin ta MoMo PSB.
Waɗanda ba su da asusun MoMo za su iya buɗe shi ta hanyar latsa *671# ko sauke manhajar MoMo NG.
Gwamnatin Tarayya ta ce ba sai mutum ya yi rajista, ya biya wani kuɗi ko ya bi ta hannun wani wakili ba kafin ya samu tallafin.
Ta kuma bayyana cewa ana biyan tallafin ne a matakai, don haka waɗanda saƙonsu ya nuna “NOT SELECTED” ba yana nufin an cire su gaba ɗaya daga shirin ba.
Domin samun ƙarin bayani ko kai ƙorafi, ana iya kiran layin kar ta kwana na NERSI ta lambar 0700-022-2222.












