ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

by Sadiq
56 minutes ago

Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi barazanar tsunduma yajin aikin gama-gari a faɗin ƙasar nan idan gwamnatin tarayya ta gaza magance buƙatun ma’aikata a taron da aka shirya gudanarwa ranar 27 ga watan Oktoba.

Matakin na zuwa ne bayan wani taro tsakanin wakilan gwamnati da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a Abuja, wanda ya ƙare ba tare da cimma matsaya ba.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce za su fara shirya ma’aikata a faɗin ƙasar domin shiga yajin aiki idan gwamnati ta gaza ɗaukar matakan da suka dace.

ADVERTISEMENT

Ga manyan buƙatu shida da ƙungiyoyin ke son gwamnati ta magance:

1. Rage farashin man fetur domin rage tsadar rayuwa ga ma’aikata.

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

2. Sake tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi da kuma fara shirin samar da sabon tsarin albashi.

3. Aiwatar da yarjejeniyar rangwamen haraji da aka amince da ita domin rage nauyin kuɗaɗen da ma’aikata ke biya.

4. Biyan bashin ƙarin albashi da sauran haƙƙoƙin da ma’aikata ke bin gwamnati.

5. Aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya (JOHESU) a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2026.

6. Biyan alawus-alawus da ma’aikatan gwamnati ke bi, ciki har da alawus na musamman da na annoba.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun buƙaci manyan jami’an gwamnati da aiwatar da waɗannan buƙatu su halarci taro na gaba domin nemo mafita.

MASU ALAKA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya
Ra'ayi Riga

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026
Labarai

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.