ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ruwan Famfo Na Daf Da Dawowa A Kano: Madalla Gwamna Abba

by Abba Anwar
3 weeks ago
Ruwan

Gagarumin aiki kan matatun ruwanmu na jihar Kano da shimfida bututu a hanyoyin ruwa da gyara matsalolin ragowar injuna dake samar da ruwan famfo mai lafiya, da Gwamna Abba Kabir Yusuf yake kammalawa, na nuni da cewar cikin ‘yan kwanaki masu zuwa kadan za a fara samun wadatar ruwan sha a Kano. Da Izinin Allah.

Hakan ke nuni da cewa ƙarni na ƙishirwa a Kano ya zo ƙarshe. Gwamna Injiniya Abba, ya mayar da tsaiko da aka yi na shekaru 95 zuwa wani sabon tarihi na zuba zunzurutun kudi har Naira Biliyan 21.3. Wannan ba magana ba ce kawai sakaka, jagoranci ne, jajircewa da kuma nuna cikakken kishin ƙasa.

Abin da ke faruwa a Kano yanzu ya cancanci duniya ta saurara. A Cape Town, sun kira ƙarancin ruwa da “Day Zero” – ranar da duniya za ta wayi gari ba ruwa. A Flint, Amurka, gubar dalma ce ta zama bala’i. Amma a Kano – birni mafi yawan jama’a a Arewacin Najeriya – abin ya zo ne a hankali, cikin shiru, amma ya fi kowanne raɗaɗi. Sama da shekaru goma, famfo ya bushe. Babu sanarwa, babu gargadi. Iska kaɗai ke fita.

ADVERTISEMENT

LISSAFI MAI BAN TSORO

Kano na buƙatar Lita Miliyan 700 a kowace rana domin ta rayu. Har zuwa bara, tana samun ƙasa da Lita Miliyan 300. Akwai gibi na Lita Miliyan 400. Wannan ba ƙaranci ba ne, rushewar tsari ce gaba ɗaya. Mata na tashi ƙarfe 4 na dare don neman ruwa a burtsatse. Yara na ɗaukar jarka suna yawo kilomita. Masana’antu sun durƙushe. Annobar kwalara ta ɓarke a lokuta bayan lokuta.

LABARAI MASU NASABA

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

Wasu gwamnatoci a baya duk da sun san ainihin matsalolin, amma sun fi amincewa da shafa garin magani wajen da a ke bukatar aikin tiyata. Wato zuciyar al’umma. Shine ruwan sha. Amma gwamnatin Abba ta zaɓi yin aikin tiyatar zuciya. Kuma yanzu zuciyar ta fara bugawa.

TARIHIN SHEKARU 95: RUHIN GARI

Labarin ruwan Kano bai fara jiya ba. Ya fara ne a 1927 a zamanin Sarki Abdullahi Bayero da Turawan mulkin mallaka suka kafa gidan ruwa na Challawa wanda shine na farko a Arewacin Najeriya. An kammala shi a 1930 da ƙarfin samar da Lita Miliyan 20.

Sai Tsohuwar Tamburawa a 1986 da ƙarfin Lita Miliyan 9.6, daga baya aka haɓaka zuwa Miliyan 20. Sai Sabuwar Tamburawa mai ƙarfin lita Miliyan 150. Kuma uwar duka, manyan ma’ajiyar Goron Dutse – guda biyar da aka gina tsakanin 1930 da 1974. Dan ajiye Lita sama da Miliyan 40. Su ne ruhin ruwan Kano.

Tsari ne da haziƙai suka tsara, amma sakaci da wawushewa suka kashe shi. Wannan lamari ya damu Gwamna tun kafin rantsuwarsa a 29 ga Mayu, 2023, har ya kafa Kwamitin Kwararru dan bincike da tattaro bayanai na yadda za a yi abinda ya kamata.

Da nake maganar wannan cigaba da a ka samu a Kano da wani aminina daga Darmanawa sai ya kada baki ya ce, “Wannan ƙoƙari ya cancanci goyon bayan kowa.”

Rahoton da wadancan kwararru su ka bayar ya so ya yi kama da rahoton bayanin abubuwan da suka faru a filin yaƙi. Rahoton da injiniyoyi suka ba Gwamna ya yi kama da na filin yaƙi.

A Challawa, yanayin da wajen ya fada an bayyana shi da “… mai ban tausayi da takaici”. Cikin manyan injinan samar da wuta ga injunan matatar ruwan guda shida, 2 ne kaɗai ke dingisawa. Matatar ruwa ta 1 da ta 2 sun mutu gaba ɗaya. Ta 3 tana numfasawa ne kawai da kashi 30% kacal.

Mafi muni, an yi awon gaba da kayan aiki. An sace famfon tuka ruwa, an cire na’urorin kunna wuta, an sace wayoyin ƙarƙashin ƙasa. Kuma abin da ya ba manyan Injiniyoyi mamaki, shine, an tono bututun ƙarƙashin ƙasa mai tsawon kilomita 15.6 da ke kawo ruwa Challawa an sace shi gaba ɗaya. Babu abinda ba a gani ba. Zamba baro – baro.

A Goron Dutse, labarin ya fi muni. Tafkunan da suka shayar da Kano kusan ƙarni ɗaya, sun yi shekaru goma babu digo ɗaya. Sun bushe, sun tsage, sun cika da yashi.

Jimillar ɓarnar ta haura Naira Biliyan 30. Wata gwamnati ta kashe Naira Biliyan 5.6 a watanni 11 don “kulawa” amma ba a canza bututu ba, ba a fitar da yashi ba, ba a sayi famfo ba. Sakamakon haka, Tamburawa da aka tsara ta bayar da Lita Miliyan 150 tana bayar da 27% kacal. Challawa ta Lita Miliyan 220 tana bayar da ƙasa da 30%. A tare ya kamata su bada Lita Miliyan 370, amma suna bada ƙasa da Lita Milyan 90. Domin a gyara Challawa kaɗai sai an kashe Dala Miliyan 10, saboda injinan na 1930 dole ne a ƙera su musamman a Turai.

Daukar abu da gaske ga shugaba irin yadda Gwamna Abba yake yi wato sam sam ba ya misaltuwa. Manyan birane ba a farfaɗo da su da surutan baka kawai. Ana farfaɗo da su da himmar shugaba ta gaskiya. Anan ne Gwamna Abba ya bambanta.

Ba tura wakili yake ba, zuwa yake da kansa. Kwanan nan, shi da Mataimakinsa, H.E. Murtala Sule Garo, sanye da takalman irin na ma’aikatan ruwan, sun zagaya Challawa da Tamburawa tare da Injiniyoyin CGC Nigeria Limited da CCECC Nigeria Limited. Haka nan sun kai irin wannan ziyara ga wajen adana ruwa na Gorondutse. Shugabanci nagari.

Saboda tsananin sanin muhimmanci da ruwa yake da shi ga rayuwa da kuma addini, hakan ya sa ya amince da zuba tsabar kudade mafi girma a harkar ruwa a Kano cikin shekaru 15 da su ka gabata. Yayin da ya sa tsabar kudi har Naira Biliyan 21.29.Ba jita-jitar Biliyan 21.89 ba. Kwangila ce da aka rattaba hannu ta Naira Bilyan 21.29.

Misali Naira Biliyan 9.9 ga CGC don gyara Tamburawa. Sai Naira Biliyan 11.39 ga CCECC don gyara Challawa da farfaɗo da Goron Dutse.

ME AKA YI A ƘASA?

Kamar yadda Kwamishinan Ruwa mai ci, Dr. Dahiru Muhammad Hashim ya tabbatar:

1. An maye gurbin bututun 15.6km na asbestos na 1970 da sabon bututun ƙarfe mai inganci zuwa Goron Dutse.

2. An fitar da yashi da gyara gaba ɗayan ma’ajiyun ruwa na Goron Dutse.

3. An gyara injinan tace ruwa (clarifiers), na’urorin tacewa da famfo masu matsa ruwa.

4. An sayo sabbin injunan famfo guda goma masu ƙarfin Kilowatt 110.

5. An kammala gwajin aiki a tsakiyar watan Satumba.

Haka kuma, cikin manyan famfon ruwa 19 na ƙauyuka da suka mutu, tara na kan hanyar dawowa. Guzugu a Kabo ta dawo, Joda a Gabasawa ta dawo, Wudil da ta mutu shekaru da yawa ta dawo da rai. A karon farko, karkarar Kano na cikin lissafi.

A ranar 21 ga Satumba, 2026, Ma’aikatar ta sanar da cewa za a fara raba ruwa mai tsafta nan da kwanaki ba masu jimawa ba.

DARASI DAGA DUNIYA

Daga Landan zuwa Legas, harkar ruwa an siyasantar da ita. Majalisar Dinkin Duniya ta ce ƙarancin ruwa zai raba mutane Miliyan 700 da muhallansu nan da 2030. Abin da Gwamna Abba ya yi darasi ne kuma babbar hobbasa ce na yadda za a juyar da akalar wannan hasashe ba tare da bashin Bankin Duniya ba, ba tare da sayar da kadarorin al’umma ba.

Bai jefa matsalar waje ba, ya biya kuɗin maganinta. Bai zargi baya ba, ya gyara gaba.

Na taba magana da Malam Musa a Tarauni yana kukan rashin ruwa. A yau da na sake tambayarsa, sai murmushi yake yi ya na cewa “Gaskiya Gwamna na iya bakin ƙoƙarinsa.”

Idan famfo a Kofar Mata ya fara tari ya ɓulɓulo, idan yaro a Dala ya sha ruwan famfo a karon farko a rayuwarsa, idan Goron Dutse ya sake cika bayan shekaru goma na fari – Kano ba ruwa kaɗai za ta yi murna ba. Za ta yi murna da Gwamnan da ya tabbatar da cewa mafarkin shekaru 95 da yashi ya binne, da bututun da aka sace, da alkawura suka gagara, na iya sake kwarara kuma a samu alfanun abin.

Wannan ba gwamnati ba ce kaɗai, daukar abu ne da dukkan muhimmanci mara jijjigewa. Daga wannan Jagora nagari.

Ruwan
Abba Anwar
+ postsBio
  • Abba Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-anwar/
    Hobbasar Gwamna Abba Kan Titunan Birnin Kano
  • Abba Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-anwar/
    Sanata Barau Da Haɗin Kan APC A Kano
  • Abba Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-anwar/
    Siyasar Kano: Akwai Buƙatar Gwamna Abba Ya Ƙara Nazari
  • Abba Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-anwar/
    Yadda Sanata Barau Ke Samar da Masana Don Ci Gaban Kano

MASU ALAKA

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya
Rahotonni

Shekaru 6 Bayan Zanga-zangar #EndSARS: Abubuwa 8 Da Suka Girgiza Nijeriya

October 20, 2026
Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya
Rahotonni

Bankin Duniya Da IMF Sun Yi Gargaɗi Kan Barazanar AI Na Rasa Ayyukan Yi A Nijeriya

October 13, 2026
Za A Ci ’Yan Siyasa Masu Kalaman Ɓatanci Tarar Miliyan 10 Da Ɗaurin Watanni 12 — INEC
Rahotonni

Jam’iyyu Da Ƴan Takara Sun Yi Wa INEC Bore Kan Cire Sunayensu Daga Takara

October 12, 2026
Next Post
Za A Wallafa Rubutaccen Jawabin Shugaba Xi Kan Bunkasa Rayuwa Da Walwalar Jama’a

Za A Wallafa Rubutaccen Jawabin Shugaba Xi Kan Bunkasa Rayuwa Da Walwalar Jama’a

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

An Yi Wa Tinubu Ihun “Ba Ma Yi” A Taron Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen APC A Kaduna

October 24, 2026
Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

Sin Ta Lashe Lambobin Yabo Mafiya Yawa A Gasar Asiya Ta 2026 Ajin Masu Bukatar Musamman

October 24, 2026
EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

EUROMATCH NPFL: Katsina United Ta Raba Maki Da Plateau United

October 24, 2026
An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Aike Da Masu Aikin Ceto Sama Da 5,000 Bayan Aukuwar Girgizar Kasa Mai Karfi A Jihar Xizang Ta Kasar Sin

October 24, 2026
Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Majalisar Dokokin Kenya, Moses Wetangula

October 24, 2026
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

‘Kana Cikin Rudu’ — Atiku Ya Mayar Wa Tinubu Martani Kan Zargin Yunwa Da Talauci

October 24, 2026
Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

Fahimtar Cikakken Zaman Kwamitin Tsakiyar JKS

October 24, 2026
Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

Tsarin Kwalliya Da Adon Manzon Allah (SAW)

October 24, 2026
2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

2027: Duk ’Yan Arewan Da Ke Takarar Shugaban Ƙasa Maƙiyan Arewa Ne – Akume

October 24, 2026
Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

Wane Irin Tasiri Sabuwar Doguwar Tafiya Za Ta Yi Wa Duniya?

October 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.