ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Siyasar Kano: Akwai Buƙatar Gwamna Abba Ya Ƙara Nazari

by Abba Anwar
4 months ago
Kano

A bayyana ne yake, abin da ya faru jiya a wurin taron bikin karɓar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa cikin jam’iyyar APC, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, wanda ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙàsa Kashim Shettima, GCON, wani ma’auni ne da yake haska wanda ya fi shiri a kan zaɓen shekara ta 2027, tsakanin gwamna da jagororin APC a Jihar Kano.

Tashin farko, idan mutum ya yi nazarin taron zai fahimci cewa; da yawa daga cikin waɗanda suka jagoranci shirya taron a ɓangaren gwamna, ko dai sun nuna sakaci da lalaci, ko suna da raunin fahimtar yadda gwagwarmayar siyasa take, ko kuma a harkar tasu akwai zunzurutun rashin ƙwarewa.

  • Siyasar Kano: Akwai Buƙatar Gwamna Abba Ya Ƙara Nazari
  • Idan Gwamna Abba Ya Ziyarci Kwalejin Bebeji Matsalarmu Za Ta Zo Ƙarshe – HOD Habib

Na yi zaton ganin dandazon masu jajayen huluna sun mamaye wurin. Kasancewar har yanzu, ita ce wani sitamfi na magoya bayan gwamnan, kafin daga nan zuwa wani lokaci a cire ta baki-ɗaya. Samun yawaitar ko ruwan masu jajayen huluna a wajen, shi ne zai nuna ƙarfin gwamnan da jama’arsa. Wanda hakan na nufin, gwamna yana tare da dandazon jama’ar da suka shiga APC tare, amma kuma sai aka samu saɓanin haka.

ADVERTISEMENT

Abubuwan da suke yawo da falfali a wajen, riguna ne da huluna na masu ɗauke da sunayen wasu jiga-jigan jam’iyyar APC. Tun kuwa daga filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano, har zuwa tituna, inda Mataimakin Shugaban Ƙàsa da manyan baƙi suka biyo a hanyarsu ta isa filin wasa na Sani Abacha, wajen taron.

Ina son tuna wa Gwamna Abba cewa; ya kamata a ce ya fi kowa tuna daga inda ya fito, sannan kuma mene ne hatsarin wajen. Wani abin da na ƙara lura da shi shi ne, da a ce alhakin wannan taron kawai an bar shi a hannun gwamna ne, shi kuma ya wakilta waɗanda ta ɓangarensa ya ba nauyin yin tasu hoɓɓasar a wajen wannan taro, da kuwa tabbas ba a samu nasarar da aka iya samu ba yanzu.

LABARAI MASU NASABA

PRP Ta Musanta Zargin Cewa Kwankwaso Ya Sayi Fom 69 Domin Kwace Jam’iyyar

Jam’iyyar APC Ta Tafka Asarar Mabiya A Gombe, Sun Bi Pantami PDP

Amma fa shi gwamna a kan kansa, ya yi iya nasa. Abin tambayar shi ne, ina mutanensa da ya ɗora musu nauyin harkar waɗanda ke cikin gwamnatin tasa?

Wannan taron babu shakka ya ƙara haska tare da tabbatarwa kowa irin tsari da tasiri da tsari na jiga-jigan APC da gwamna ya tarar a jam’iyyar suke. Ko ina ka kalla, abin da kawai za ka gani su ne magoya baya nata taken alƙiblar siyasarsu. Kuma kashi 80 cikin 100 na magoya bayan da suka fito, daga ɓangaren manyan jam’iyyar APC suke.

Har ta kai ta kawo fa da yawa mutane sun fara tambayar cewa, ina shugabannin ƙananan hukumomi? Ina kwamishinoni da mashawartan gwamna? Ina Ƴan majalisar da gwamna ya tawo da su, daga na jiha zuwa na tarayya? Ina makusantan gwamnan? Ina masu yi wa gwamnan fatan alhairi? Ina shugabannin ɓangarorin hukumomin gwamnati? An yi waɗannan tambayoyin ne saboda ba a ga ɓurɓushinsu yadda ya kamata ba.

Wannan sakacin, na nuna rashin kyakkyawan shirin wayar da kai daga ɓangaren shugabannin ƙananan hukumomi, musamman, waɗanda bisa tsari da ake da shi ya kamata su taka gagarumar rawa wajen haɗa jama’a daga ƙananan hukumominsu. Wato daga tushe.

Allah Ya ji ƙan Murtala Sule Garo, ba don ya mutu ba. Sai nake tuna lokacin yana Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (ALGON), ko lokacin da yana matsayin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, ko lokacin da yake matsayin Sakataren Tsare-tsaren Jam’iyya mai mulki a lokacin. Tafiyar tasa akwai kyakkyawan haske, tsafta, tsari, jajircewa da kuma cika alƙawura.

Ni a wajena, taron nan da aka yi ya bayyana ƙarfi, tasiri da darajar mutane huɗu ko biyar da na ga jajircewarsu a lokacin taron. Abin da nake nufi shi ne, su waɗannan mutanen na APC, waɗanda Gwamna Abba ya tarar a jam’iyyar a wannan lokacin da aka samu juyawar yanayin siyasar a Jihar Kano.

Su ne, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Ta Ƙasa, Sanata Barau I Jibrin, CON, Mataimakin Ɗan Takarar Gwannan Kano na Jam’iyyar APC, a zaɓen shekara ta 2023, Murtala Sule Garo, Shugaban Kwamitin Raba Arziƙin Ƙasa na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Bichi, Babban Daraktan Cibiyar Nagartar Ayyuka Ta Ƙasa, Baffa Babba Dan Agundi da wakilin al’ummar Ƙananan Hukumomin Tudun Wada da Doguwa a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Alhassan Ado Doguwa.

Waɗannan mutane da na ambata, da hoɓɓasar da suka yi a lokacin taron, sun tabbatar wa da ƴan Nijeriya cewa; jam’iyyar APC har yanzu a raye take, kuma tana motsawa sosai a Jihar Kano.

Sannan wannan wani saƙo ne da aka aika wa Shugaban Ƙàsa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, cewa; tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, CFR, har yau har gobe tsayayye ne, kuma bai yi ƙasa a gwiwa ba.

Gudunmawar da mutanen nan biyar masu ƙima da na ambata a sama suka bayar, ya kamata ya zama wata izina ga gwamna, domin ya san su wa ya kamata ya ƙara riƙewa a jihar. Dukkaninsu sun ba da gagarumar gudunmawa, sun kuma nuna dabarun siyasa, ƙwarewa da yin aiki da gwamna bisa jajircewa, kan abin da za a yi a lokacin da ya kamata.

Don haka, samun nasara da matakan samun nasarar, sau da yawa a hannun gwamna suke. Idan na yi maganar nasara, ina hangen shekara ta 2027.

Idan na tawo ƙasa, bayan bayyana sunayen Barau, Garo, Abba Bichi, Doguwa da Dan Agundi, sai na kalli tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Birni da Kewaye, Fa’izu Alfindiki da Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labarai na yanzu, Abdullahi Waiya, waɗanda su ma sun yi abin da ya dace, sun yi aiki ƙwarai da gaske a ɓangarensu.

Na yi matuƙar jinjina wa ƙoƙarinsu, jajircewa da cikakkiyar biyayya da suka nuna, tun kafin ma taron da lokacin taron da bayan taron. Kazalika, na jinjina wa kyakkyawan aikinsu a matsayin ƴan wasan da ake buƙata.

Idan na ƙara tawowa ƙasa dai, dole a yaba wa jajircewa, biyayya da goyon bayan Kwamared Magaji Kabiru Gulu daga Rimin Gado da kuma wannan matashin Aminu Dahiru, shi kuma daga Ƙaramar Hukumar Gwale. Idan kuma ana maganar haɗa gangami na mutane, ina da yaƙinin za su bayar da gagarumar gudunmawa daban-daban.

Ina bayar da shawara ga mai girma Gwamnan Jihar Kano, Yusuf, da ya yi duban tsanaki a cikin shugabannin ƙananan hukumominsa 44. Ta bayyana ƙwarai cewa, akwai gazawa matuƙa ta fuskar hada-hadar shirya gagarumin taro irin wanda ya wakanan.

A jama’arka a wajen wannan taro, mai girma gwamna gaskiya akwai naƙasu, rashin ƙwarewa, sakaci, riƙon sakainar kashi, kan rashin shigar da jama’a cikin al’amura. Yayin da gwamna ya kamata ya fuskanci ƙalubalen da ke gabansa da gasken gaske, yin aiki da jama’ar APC, ya zama abin da bai kamata a kaucewa ba.

 

 

 

Kano
Abba Anwar
+ postsBio
  • Abba Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-anwar/
    Hobbasar Gwamna Abba Kan Titunan Birnin Kano
  • Abba Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-anwar/
    Sanata Barau Da Haɗin Kan APC A Kano
  • Abba Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/abba-anwar/
    Yadda Sanata Barau Ke Samar da Masana Don Ci Gaban Kano

MASU ALAKA

2023: Gwarazan Jam’iyyu A Karon Battar Zaben Shugaban Kasa
Siyasa

PRP Ta Musanta Zargin Cewa Kwankwaso Ya Sayi Fom 69 Domin Kwace Jam’iyyar

June 22, 2026
Jam’iyyar APC Ta Tafka Asarar Mabiya A Gombe, Sun Bi Pantami PDP
Siyasa

Jam’iyyar APC Ta Tafka Asarar Mabiya A Gombe, Sun Bi Pantami PDP

June 22, 2026
ADC Ta Sake Tabbatar Da Ibrahim Khalil A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano Na 2027
Siyasa

ADC Ta Sake Tabbatar Da Ibrahim Khalil A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano Na 2027

June 21, 2026
Next Post
Sakamakon Matsin Lambar Jami’an Tsaro, ‘Yan Ta’adda Na Fuskantar Ƙarancin Abinci

Sakamakon Matsin Lambar Jami'an Tsaro, 'Yan Ta'adda Na Fuskantar Ƙarancin Abinci

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

June 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

June 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 57 Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta’addanci A Adamawa

June 23, 2026
Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.