Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya faɗa wa sashen Hausa na BBC cewa, sata aka je yi gidansa bayan gwamnatin jihar ta ce ta ƙwato wasu motoci daga gidan nasa da gwamnan ya ƙi mayarwa gidan gwamnati.
A ranar Juma’a ne gwamnatin Zamfara Æ™arÆ™ashin jagorancin Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ta ce jami’an tsaro sun shiga gidajen Matawallae biyu, a Gusau da kuma Maradun, inda suka Æ™wato motoci har 40.
- Bello Matawalle Ya Wawashe Kudi Da Motocin Gwamnati — Gwamnatin Zamfara
- ‘Yansanda Sun Kai Samame Gidan Matawalle, Sun Kwace Motoci 4
Sai dai Matawalle ya ce “sakarci ne” da “talauci” ya sa aka shiga gidan nasa, yana mai cewa an sace kayayyaki ciki har da hijabin matansa.
“Dukkan É—akunan matana babu wanda ba a shiga ba, har da hijabi na mata aka kwashe. Hatta irin murhun nan na garwashi, duka an saka cikin mota an tafi da su,” in ji shi.
Ya Æ™ara da cewa wasu daga cikin motocin da aka kwashe ya saye su ne daga Amurka tun kafin ya zama gwamna saboda da ma sana’arsa ce sayar da motoci.