Babban Sakataren Majalisar Shari’a Ta Nijeriya (SCSN), Nafiu Baba-Ahmed, ya rasu bayan fama da doguwar jinya.
Wani ɗan uwansa, Aminu Baba-Ahmed ne, ya sanar da rasuwarsa a wani saƙo da ya wallafa a Facebook ranar Talata.
Ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, tare da roƙon Allah Ya gafarta masa kurakuransa, Ya kuma sa Aljanna ce makomarsa.
A cewar iyalan mamacin, za a yi sallar jana’izarsa a Masallacin Ƙasa da ke Abuja bayan sallar Azahar.
Baba-Ahmed lauya ne, kuma ya kasance Sakataren Janar na SCSN, majalisar da ke fafutukar inganta fahimta da aiwatar da ƙa’idojin Shari’a a Nijeriya.
An haifi Baba-Ahmed a shekarar 1956, kuma ya rasu ya bar matansa da ’ya’yansa.
Iyalan mamacin sun buƙaci jama’a da su sanya shi a cikin addu’o’insu.














