Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Rt. Hon. Bilyaminu Moriki, ya ce ƙofar Majalisar a buɗe take ga ’yan majalisar takwas da aka dakatar, idan suka nemi afuwa kan laifukan da aka zarge su da aikatawa.
Wannan na zuwa ne bayan ’yan majalisar takwas da aka dakatar suka fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC a ranar Asabar da ta gabata.
An dakatar da ’yan majalisar ne a ranar 26 ga watan Fabrairu, 2024, bayan zarge-zargen aikata wasu laifuka da suka haɗa da almundahana, rashin ɗa’a, haɗin baki, ɓarna, raina majalisar.
Da yake magana kan batun, Kakakin Majalisar ya ce ana zargin ’yan majalisar da aikata wasu abubuwa da suka shafi almubazzarancin kuɗi, shiga ofisoshin majalisa da ƙarfi da kuma lalata dukiyar gwamnati.
Ya ƙara da cewa daga cikin zarge-zargen da ake musu akwai lalata ofishin Akawun Majalisa, lalata kayayyakin Majalisa, shiga zauren Majalisa ba bisa ƙa’ida ba, tare da gudanar da zaman da ba a amince da shi ba.
A cewar Moriki, girman zarge-zargen da sauran batutuwan da ke da alaƙa da su ya kai ga shigar da ƙara a gaban kotu.
Dangane da sauya shekar ’yan majalisar zuwa jam’iyyar ADC, Kakakin ya ce matakin ba zai sauya matsayin Majalisar kan batun ladabtarwar da aka yi musu ba.
Ya bayyana sauya sheƙar a matsayin wani yunƙuri na karkatar da hankalin jama’a daga ainihin batun da ya shafi dalilan dakatar da su, yana mai cewa hakan ba zai sa Majalisar ta yi watsi da matakan da ta ɗauka ba.
Sai dai ya jaddada cewa ƙofar Majalisar a buɗe take ga ’yan majalisar idan suka nemi afuwa kan laifukan da aka zarge su da aikatawa.
Moriki ya kuma tabbatar wa jama’a, musamman magoya bayan jam’iyyar APC, cewa Majalisar Dokokin Jihar Zamfara tana nan daram, tana gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.














