A yau Juma’a 23 ga watan Oktoba ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin MOC ta gabatar da rahoton yadda kasuwar cinikayya ta kasar ta gudanar da ayyukanta, a watanni tara na farkon shekarar nan, inda ta lura cewa, matakan bunkasa amfani da kayayyaki da aka dauka suna fadada kasuwar cinikayyar kayayyaki, sannan tsarin sayayyar kayayyaki daga mazauna kasar na ci gaba da bunkasa.
A cewar rahoton, a watanni 9 na farkon shekarar nan, matsakaicin amfani da kayayyaki da mazauna kasar suka yi ya kai Yuan 22,000 wanda ya dara na shekarar bara da kaso 3.6. Hakikanin ci gaban da aka samu bayan tasirin sauyin farashin kayayyaki ya kasance a kan maki 2.7 cikin dari, yayin da cinikayyar kayayyaki da ake sayarwa kai tsaye ga masu amfani ya karu da kaso 2.6 cikin dari sama da na shekarar bara. Kazalika cinikayyar hidimomi kai tsaye ga masu amfani ya samu tagomashi da karin kaso 5.0 cikin dari.
Jimillar hada-hadar sayen kayayyaki ya bayar da gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin da kaso 46.7 cikin dari wanda ya haifar da bunkasar ma’aunin GDP da kaso 2.1 cikin dari. (Suleiman Suleiman)













