Wakilin Sin na dindindin a MDD Fu Cong, ya yi jawabi jiya 22 a babban taron MDD kan batun gyare-gyaren kwamitin sulhu, inda ya jaddada cewa makasudin gyare-gyaren da ake sa ran yi wa kwamitin sulhu shi ne, canja halin da kwamitin ke ciki na ba da karfin wakilcin kasashe masu wadata a kwamitin fiye da kima.
Fu Cong ya ce, Sin na goyon bayan kwamitin sulhu ya yi gyare-gyare da suka wajaba kuma masu ma’ana domin kara karfin iko da ingancinsa, da kara karfin fuskantar rikice-rikice da kalubale, da gudanar da aikin da kundin tsarin MDD ya dora masa.
Fu Cong ya gabatar da shawarwari guda 3, wadanda suka kunshi, na farko, dole ne a mai da hankali kan kara karfin kasashe masu tasowa a kwamitin a fannin wakilci da damar yin magana. A ba da dama ga kasashe masu tasowa da ke da ‘yancin kai a manufofin harkokin waje, da kananan da matsakaitan kasashe, wajen shiga aikin yanke shawara a kwamitin, musamman a gyara kuskuren da aka yi wa Afirka a tarihi, da kuma amsa bukatun Afirka bisa manufar karamci.
Na biyu, dole ne a mutunta yarjejeniyar kasashe mambobin kungiyar, da kuma dagewa kan warware batutuwa daga tushe. Idan a samar da “shirin gyare-gyare iri daya” cikin gaggawa kafin bangarorin da abin ya shafa su cimma cikakkiyar matsaya daya, hakan zai kara tsananta sabanin ra’ayi da rikice-rikice tsakanin bangarorin.
Na uku, a tabbatar da cewa tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnatoci ita ce kadai halastacciyar turbar da mambobin kasashen majalisar ke bi wajen tattauna batun gyare-gyaren kwamitin, kuma ya zama ba za a iya maye gurbin rawar da take takawa ba.(Amina Xu)













