Shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu da ke Jihar Zamfara, Honarabul Nura Umar Abdullahi, tare da wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su, sun kuɓuta daga hannun ƴan ta’adda bayan sun shafe kwanaki 61 a tsare.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya bayyana cewa dakarun sojoji sun karɓi mutanen a yankin Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda da sanyin safiyar ranar Alhamis, bayan sun tsere a yayin wani sumame da sojoji suka kai maɓoyar ƴan bindigar.
An sace Honarabul Abdullahi ne a gidansa da ke garin Bungudu a ranar 25 ga Yulin 2026, inda a yayin wannan hari ƴan bindigar suka kashe jami’an tsaronsa huɗu, da suka haɗa da ƴansanda biyu da kuma ƴan banga biyu.
Sanarwar ta ƙara da cewa an garzaya da mutanen zuwa asibitin sojoji domin duba lafiyarsu da karɓar muhimman bayanan sirri, inda a yanzu haka aka riga aka haɗa ɗaya daga cikinsu da iyalansa, yayin da ake shirye-shiryen miƙa sauran ga iyalansu da gwamnatin jihar.
A ƙarshe, rundunar sojin ta yaba da juriya da ƙarfin halin waɗanda suka kuɓutar, tana mai tabbatar da ci gaba da kai hare-hare domin fatattakar ƴan ta’adda a yankin baki ɗaya tare da yin kiran neman goyon bayan al’umma da sahihan bayanai.














