Shugaban kasar Mozambique, Daniel Francisco Chapo, ya ce aikin gona yana da matukar muhimmanci ga Mozambique, don haka yana fatan kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasarsa da Sin a wannan fanni, da nufin kara karfin samar da hatsi a Mozambique.
Shugaba Chapo ya bayyana haka ne ranar Asabar a lardin Gaza na Mozambique, lokacin da ya halarci bikin girbin alkama a gonar Wanbao Mozambique da Asusun Bunkasa Sin da Afirka ya zuba jari a ciki. A cikin gonar, shugaba Chapo ya duba shinkafa, alkama, masara da sauran amfanin gona, da kuma iri, sannan ya fahimci yadda aikin ke hada kai da manoman yankin.
Ya bayyana cewa yana fatan a yayata wannan tsarin hadin gwiwar noma zuwa wasu karin yankuna na Mozambique.
Gonar ta Wanbao Mozambique ta fara aiki a kasar Mozambique ne tun daga shekarar 2012, inda take noman wasu amfanin gona, ciki har da shinkafa, alkama, masara da dai sauransu a lardin Gaza.
Kuma a kowace shekara, tana gudanar da hadin gwiwa da iyalan manoma kimanin 350 zuwa 400 a yankin, ta hanyar shigar da ingantattun iri da yayata fasahar noma, da samar da injinan noma da jagorantar aikin noma, da sauransu, don taimaka wa manoman da ke hadin gwiwa da ita, kara samun amfanin gona. (Bilkisu Xin)














