Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki a Amurka, shugaban majalisar bunkasa kasuwanci tsakanin Amurka da Sin, Sean Stein ya yi tsokaci game da muhimmancin da raya dangantakar Sin da Amurka cikin kwanciyar hankali da aminci da dorewa ke da shi ga kasashen duniya.
Sean Stean ya yi tsokacin ne yayin wata hira da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin (CMG), inda yake cewa, kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Amurka ba kasashen biyu kadai za ta amfanawa ba, za ta kuma kawo tabbaci ga kasashen da ke fadin duniya. Ya ce ko kasashen ASEAN ko kasashe maso tasowa da kasashen Turai ko Latin Amurka, duk za su san yadda za su yi hulda da Sin da Amurka a lokaci guda.
Baya ga haka, babu wata kasa da ke son goyon bayan wani bangare, domin kowace tana da moriya a hulda da dukkan kasashen watau Sin da Amurka. Ya ce samun dangantaka mai kwanciyar hankali tsakanin Sin da Amurka, zai ba kasashe damar neman cimma muradunsu da kansu da kuma samun alfanu daga hulda da Sin da Amurka. (Fa’iza Mustapha)














