Shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan, ta kaddamar da tashar samar da lantarki daga ruwa ta Julius Nyerere mai karfin megawatt 2,115, wanda ke zaman wani katafaren aiki da ake sa ran zai karfafa samar da wutar lantarki da gaggauta raya ayyukan masana’antu da harkokin tattalin arziki a kasar.
Zhang Rui, manajan ayyuka na kamfanin PowerChina ya bayyana cewa, tashar wadda kamfanonin PowerChina da Dongfang Electric na kasar Sin suka shiga aikin gina ta, na da karfin samar da lantarki megawatta 2,115. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
ADVERTISEMENT














