Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya shugabanci taron manema labaru da aka gudanar a yau Alhamis 10 ga wannan wata, game da ganawar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da jakadan Amurka dake kasar Sin suka yi, da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, Guo Jiakun ya bayyana cewa, diplomasiyyar dake tsakanin shugabannin kasashen biyu tana taka muhimmiyar rawa, a fannin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, kana bangarorin biyu suna wanzar da mu’amala kan shirin ganawar da manyan shugabannin kasashen biyu za su yi a bana.
Game da matakin Amurka na kafa dandalin tabbatar da asali, da hanyoyin samar da hidimomi ta fasahar AI na duniya na farko a kasar Panama, Guo Jiakun ya bayyana cewa, fasahar AI tana da nasaba da makomar bai daya ta dan Adam. Don haka ya kamata bangarori daban daban su bi ka’idojin bude kofa, da yin hadin gwiwa, da samun moriyar juna, da kuma neman buri mai kyau a wannan fanni.
Ya ce kafa rukunin musamman, da kin yin hadin gwiwa tare da saura, da siyasantar da yankuna daban daban, batu ne da zai yi mugun tasiri ga kasashe masu tasowa na duniya, ciki har da na Latin Amurka, da Caribbean wajen bunkasa fasahohin zamani.
Jami’in ya kara da cewa kasar Sin tana son yin kokari tare da bangarori daban daban, ciki har da na Latin Amurka, da Caribbean, wajen kafa tsarin sarrafa harkokin fasahar AI na duniya, mai adalci, da dacewa, don sa kaimi yadda fasahar AI za ta amfani al’ummun kasa da kasa. (Zainab Zhang)














