Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa dalibai a Nijeriya za su fara samun 100MB na data kyauta a kullum daga ranar 1 ga Oktoba, 2026, domin amfani da manhajojin koyarwa da shafukan intanet da aka amince da su.
Shirin, wanda Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ke aiwatarwa tare da haɗin gwiwar kamfanonin sadarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, zai fara ne da ɗaliban manyan makarantun sakandare na gwamnati da kuma manyan makarantun gaba da sakandare.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana ranar fara shirin a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da shirin a Abuja.
Ya ce shirin na daga cikin matakan gwamnati na sauƙaƙa wa ɗalibai samun damar amfani da albarkatun ilimi na zamani da kuma inganta koyon karatu ta hanyar fasahar sadarwa.
ADVERTISEMENT














