ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, October 29, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sirrin Karbuwar Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta GGI

by CGTN Hausa
5 hours ago
GGI

Idan ba mu manta ba a kwanakin baya shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wata wasika ga dandalin tattauna batutuwan jagorancin duniya na Xiong’an, wadda a ciki ya kara fayyace muhimmancin dake tattare da aiwatar da sauye-sauye da inganta tsarin jagorancin duniya, da ma saita alkibla don ingiza aiwatar da shawarar inganta jagorancin duniya ta GGI. Ko shakka babu, wannan wasika ta shugaba Xi, ta sake jaddada aniyar kasar Sin ta sauke nauyin dake wuyanta na aiki tukuru, tare da sauran kasashen duniya wajen gina duniya mai karin adalci da daidaito.

A shekarar 2025 ne shugaba Xi ya gabatar da shawarar GGI, wadda ta kasance waraka ga tarin matsalolin da duniya ke fuskanta, a fannin cike gibin jagoranci, da gina makoma ta gari ga bil’adama. A cikin shekara daya kacal, shawarar GGI ta yi matukar samun karbuwa daga kasashe da hukumomin kasa da kasa sama da 160. Kazalika, sama da kasashe 60 sun shiga kawancen shawarar ta GGI. Har ila yau, an shigar da manyan ginshikanta cikin kundin kungiyoyin kasa da kasa irinsu G20, da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO da kungiyar BRICS.

Cikin shekara guda, shawarar GGI tana kara samun karbuwa, tasirinta na kara fadada, kana shawarar ta zamo muhimmin ra’ayi da sassan kasa da kasa ke kara amincewa da ingancinta. Wadannan sassa na kara rungumar shawarar GGI a matsayin turbar kyautata cudanyar bangarorin kasa da kasa, suka kallonta a matsayin garkuwa ga manufar tabbatar da gaskiya da adalci, yayin da ake tunkarar kalubalen dawowar manufofin nuna karfin tuwo da danniya a duniya. Ga al’ummu masu yawa, shawarar GGI na samar da kyakkyawar turba ta raba ci gaban bai daya, da tsaro, da tabbaci da ake bukata a wannan duniya mai fama da yanayi na tangal-tangal.

ADVERTISEMENT

Alal hakika, managarcin tsarin jagorancin duniya na taimakawa wajen cimma moriyar bai daya ta dukkanin kasashe, kuma wajibi ne daukacin sassan kasa da kasa su yi aiki tare wajen cimma wannan buri. Kasar Sin ta shirya tsaf wajen yin aiki tare da daukacin bangarori don daga tunanin inganta jagorancin duniya ta hanyar gudanar da tuntuba mai ma’ana, da hada hannu wajen bayar da gudunmawa don cimma moriyar bai daya, da gina karfin tunkarar kalubale bisa hadin gwiwa.

A yau, sassan kasa da kasa na da alhakin yin hadin gwiwa don ingiza aiwatar da wannan shawara ta GGI, kana da wanzar da tabbaci, da karsashin cimma nasarar zaman lafiya mai dorewa a wannan duniya mai fuskantar sauye-sauye da tangal-tangal, tare da aiki bai daya domin gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama karkashin wannan muhimmiyar shawara. (Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa

Sin Ta Fadada Kasuwanci Ga ‘Yan Kasashen Waje A Kasuwar Cinikayya Cikin ‘Yanci Mafi Girma A Duniya

GGI
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Ya Kamata Tashar TBS Ta Japan Ta Tuba Ba Wai Bayar Da Uzuri Ba
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Hadin Gwiwar Fasahar AI Tsakanin Sin Da Afirka: Gani Ya Kori Ji

MASU ALAKA

Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa
Daga Birnin Sin

Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa

October 29, 2026
Sin Ta Fadada Kasuwanci Ga ‘Yan Kasashen Waje A Kasuwar Cinikayya Cikin ‘Yanci Mafi Girma A Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Ta Fadada Kasuwanci Ga ‘Yan Kasashen Waje A Kasuwar Cinikayya Cikin ‘Yanci Mafi Girma A Duniya

October 29, 2026
Ya Kamata Tashar TBS Ta Japan Ta Tuba Ba Wai Bayar Da Uzuri Ba
Daga Birnin Sin

Ya Kamata Tashar TBS Ta Japan Ta Tuba Ba Wai Bayar Da Uzuri Ba

October 29, 2026
Next Post
Yadda Cristiano Ronaldo Ya Zama Na Farko A Zaɓen Mafi Kyawun Ballon d’Or A Tarihi

Yadda Cristiano Ronaldo Ya Zama Na Farko A Zaɓen Mafi Kyawun Ballon d’Or A Tarihi

LABARAI MASU NASABA

Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

October 29, 2026
Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa

Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa

October 29, 2026
NLC Ta Buƙaci Ƴan Jarida Su Tursasa Ƴan Siyasa Kan Mafi Karancin Albashi

NLC Ta Buƙaci Ƴan Jarida Su Tursasa Ƴan Siyasa Kan Mafi Karancin Albashi

October 29, 2026
Sin Ta Fadada Kasuwanci Ga ‘Yan Kasashen Waje A Kasuwar Cinikayya Cikin ‘Yanci Mafi Girma A Duniya

Sin Ta Fadada Kasuwanci Ga ‘Yan Kasashen Waje A Kasuwar Cinikayya Cikin ‘Yanci Mafi Girma A Duniya

October 29, 2026
Ya Kamata Tashar TBS Ta Japan Ta Tuba Ba Wai Bayar Da Uzuri Ba

Ya Kamata Tashar TBS Ta Japan Ta Tuba Ba Wai Bayar Da Uzuri Ba

October 29, 2026
Yadda Cristiano Ronaldo Ya Zama Na Farko A Zaɓen Mafi Kyawun Ballon d’Or A Tarihi

Yadda Cristiano Ronaldo Ya Zama Na Farko A Zaɓen Mafi Kyawun Ballon d’Or A Tarihi

October 29, 2026
Sirrin Karbuwar Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta GGI

Sirrin Karbuwar Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta GGI

October 29, 2026
Hadin Gwiwar Fasahar AI Tsakanin Sin Da Afirka: Gani Ya Kori Ji

Hadin Gwiwar Fasahar AI Tsakanin Sin Da Afirka: Gani Ya Kori Ji

October 29, 2026
Wasan Kwaikwayo Da Ba Shi Da Tushe Na Japan Yana Yunkurin Shafa Wa Kasar Sin Kashin Kaji

Wasan Kwaikwayo Da Ba Shi Da Tushe Na Japan Yana Yunkurin Shafa Wa Kasar Sin Kashin Kaji

October 29, 2026
’Yansanda Sun Kama Tsohon Gwamnan Imo Rochas Okorocha A Abuja

Kotu Ta Tabbatar Da Rochas Okorocha A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Na Imo Ta Yamma

October 29, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.