Idan aka kwatanta jam’iyyar siyasa da wani babban itace, to, yi wa kanta kwaskwarima zai kasance fuskantar matsalolin dake faruwa a cikin jikin itacen, da cire abubuwa masu kawo illa ga itacen don kiyaye lafiyarta baki daya. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da tunanin yi wa kai kwaskwarima ga jam’iyyar, wanda shi da tunanin bai wa jama’a damar sa-ido kan harkokin mulki da shugaban kasar Sin na farko Mao Zedong ya gabatar, sun kasance amsar kawo karshen rikici da yake-yake a kasar Sin, da kuma yadda za a daidaita matsaloli da kiyaye karfin jam’iyyar kwaminis ta Sin yayin da take aiwatar da harkokin kasar a dogon lokaci.
Akwai matakai hudu da za a dauka wajen yi wa kai kwaskwarima da suka kunshi: kawar da masu cin hanci da rashawa, da kyautata tsarin jam’iyyar bisa warware matsalolin da aka samu, da yin watsi da tsohon tsarin da ya wuce, da kuma inganta sabon tsarin jam’iyyar don daukar nauyin tafiyar da harkokin kasa yadda ya kamata.
Ya kamata jam’iyyar dake kan mulkin kasar ta san hadarin tinkarar kalubalen da za su kunno kai, kana ta kasance tana da karfin daidaita matsalolin da aka samu. Wannan ne muhimmin abu wajen kiyaye karfin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ya kasance wata muhimmiyar hanya wajen daidaita mawuyacin halin da jam’iyyun siyasa na kasa da kasa suke fuskanta yayin da suke aiwatar da harkokin kasa. (Zainab Zhang)














