Kwanan nan gidan talabijin na TBS na kasar Japan ya nuna wasan kwaikwayo mai suna “Vivant” karo na biyu, wanda ya samu masu kallo da yawa, sai dai labarin wasan ba shi da tushe ko kadan.
A cikin wasan an kirkira wata “kungiyar sirri ta kasar Sin” wacce a yanzu ake ganin “ta koma baya”, kuma an kwatanta ta da hukumomin leken asiri na Japan da ake ganin sun ci gaba. Bugu da kari, a cikin wasan an tsara wani yanayi inda jami’an leken asirin kasar Sin suka rika yanke yatsu da huda cikin jami’an leken asirin Japan, wadanda tamkar irin matakan azabtarwa ne da sojoji mahara na Japan suka yi wa mayakan gwagwarmayar kasar Sin a yayin yakin duniya na biyu. Wasan ya gurbata gaskiya, har ma ya dora laifukan da maharan kasar Japan suka aikata a tarihi a kan alummar Sinawa na zamanin yanzu, a yunkurin haifar da kiyayya a tsakanin sassa biyu.
A shekarun baya-bayan nan, Japan ta kirkiri wani abu da ta kira wai ” barazanar kasar Sin” don neman gyaran kundin tsarin mulki, da kara jan damarar sojoji. To sai dai kuma, a kwanakin baya tsohon firaministan Japan Shigeru Ishiba ya fadi gaskiya, inda ya ce, “Babu wani abu wai shi ‘kasar Sin ta kai hari ga Japan’, alal hakika Japan ce ta tayar da yakin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin mutane.”
Irin wadannan muryoyin da ke cikin Japan, idan aka nutsar da su a cikin karyar da masana’antun nishadi ke kitsawa, to “sake barkewar yaki” ba zai zama zato kadai ba.Bugu da kari, shugaban gidan talabijin na TBS na Japan Ryuho Masamine, yayin da yake mayar da martani ga sukar da kafofin watsa labarai na Sin suka yi kan wasan kwaikwayon, ya ce wannan aikin nishadi ne wato “cikakkiyar kirkira”, kuma ba ya aikewa da sakon da ke wulakanta wata kasa takamaimmiya ko bata ran al’ummarta. Game da wannan, da yawa daga cikin masu amfani da intanet na Japan, sun bayyana cewa wannan hujja ce duba da yadda wasan ya ambaci sunan kasar da aka mayar a matsayin abokiyar gaba.














