ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, October 29, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

by Abubakar Sulaiman
1 hour ago

Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya ta tura sabuwar bataliya da rundunar manyan makamai zuwa Jihar Kano domin ƙarfafa tsaro da inganta martanin rundunar ga sabbin barazanar tsaro. Rundunar ta ce kafa waɗannan rukunonin sojoji na daga cikin matakan faɗaɗa ayyukanta da inganta tsarin tsaron ƙasar.

Kwamandan Runduna ta Ɗaya ta Sojin Ƙasa kuma Kwamandan sashi na Ɗaya na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma, Manjo-Janar Abubakar Sadique Muhammad Wase, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar tantance ayyukan sojoji a ranar 28 da 29 ga Oktoba, 2026. Ya ziyarci Bataliya ta 24 da ke Tudun Wada da Rundunar Makamai ta 311 da ke Dambatta, a Jihar Kano.

A cewar wata sanarwa da Kakakin Hulɗa da Jama’a na Runduna ta Ɗaya, Kanal Abubakar Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis, Wase ya ce sabbin rukunonin sojojin na buƙatar jajircewa, da juriyar aiki da isasshen tallafi domin cimma manufofin da aka kafa su a kai.

ADVERTISEMENT

Ya kuma tabbatar wa sojojin cewa rundunar tana aiki tare da Gwamnatin Jihar Kano domin taimaka wa rukunonin su fara gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Wase ya ƙara da cewa jin daɗin jami’an soji da samar musu da kayan aiki da sauran tallafin gudanar da ayyuka na daga cikin abubuwan da rundunar ke ba fifiko.

Janar ɗin, wanda ya samu rakiyar Kwamandan Birged ta Uku, Birgediya-Janar Saka Jimoh, ya kuma gana da shugabannin ƙananan hukumomin Dambatta da Tudun Wada.

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Umarci Uzodinma Ya Daina Kiran Kansa Ɗan Takarar APC Na Sanatan Imo Ta Yamma

INEC: Matsayin Takarar Pantami, Gwarzo Da Adebutu; Wane Sakamako Ne Zai Iya Biyo Baya?

Ya buƙaci al’ummomin yankunan da su ba sojojin haɗin kai da goyon baya domin ƙarfafa tsaro a faɗin jihar.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    NLC Ta Buƙaci Ƴan Jarida Su Tursasa Ƴan Siyasa Kan Mafi Karancin Albashi
  • Abubakar Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Biyan Tallafin Sufuri Ga Ma’aikata Naira 70,000 A Duk Wata
  • Abubakar Sulaiman
    ADC-PCC Ta Nemi Majalisa Ta Yi Fatali Da Bashin Tinubu Na Dala Biliyan 20 Da Fam Biliyan Ɗaya
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Buƙatar Ciwo Bashin Tinubu

MASU ALAKA

Kotu Ta Umarci Uzodinma Ya Daina Kiran Kansa Ɗan Takarar APC Na Sanatan Imo Ta Yamma
Manyan Labarai

Kotu Ta Umarci Uzodinma Ya Daina Kiran Kansa Ɗan Takarar APC Na Sanatan Imo Ta Yamma

October 29, 2026
INEC: Matsayin Takarar Pantami, Gwarzo Da Adebutu; Wane Sakamako Ne Zai Iya Biyo Baya?
Siyasa

INEC: Matsayin Takarar Pantami, Gwarzo Da Adebutu; Wane Sakamako Ne Zai Iya Biyo Baya?

October 29, 2026
Tinubu Zai Tafi Saudiyya Domin Yi Wa Nijeriya Addu’a
Manyan Labarai

Tinubu Zai Gabatar Da Kasafin Kuɗin 2027 Kafin Ƙarshen Shekara

October 29, 2026

LABARAI MASU NASABA

Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

October 29, 2026
Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa

Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa

October 29, 2026
NLC Ta Buƙaci Ƴan Jarida Su Tursasa Ƴan Siyasa Kan Mafi Karancin Albashi

NLC Ta Buƙaci Ƴan Jarida Su Tursasa Ƴan Siyasa Kan Mafi Karancin Albashi

October 29, 2026
Sin Ta Fadada Kasuwanci Ga ‘Yan Kasashen Waje A Kasuwar Cinikayya Cikin ‘Yanci Mafi Girma A Duniya

Sin Ta Fadada Kasuwanci Ga ‘Yan Kasashen Waje A Kasuwar Cinikayya Cikin ‘Yanci Mafi Girma A Duniya

October 29, 2026
Ya Kamata Tashar TBS Ta Japan Ta Tuba Ba Wai Bayar Da Uzuri Ba

Ya Kamata Tashar TBS Ta Japan Ta Tuba Ba Wai Bayar Da Uzuri Ba

October 29, 2026
Yadda Cristiano Ronaldo Ya Zama Na Farko A Zaɓen Mafi Kyawun Ballon d’Or A Tarihi

Yadda Cristiano Ronaldo Ya Zama Na Farko A Zaɓen Mafi Kyawun Ballon d’Or A Tarihi

October 29, 2026
Sirrin Karbuwar Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta GGI

Sirrin Karbuwar Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta GGI

October 29, 2026
Hadin Gwiwar Fasahar AI Tsakanin Sin Da Afirka: Gani Ya Kori Ji

Hadin Gwiwar Fasahar AI Tsakanin Sin Da Afirka: Gani Ya Kori Ji

October 29, 2026
Wasan Kwaikwayo Da Ba Shi Da Tushe Na Japan Yana Yunkurin Shafa Wa Kasar Sin Kashin Kaji

Wasan Kwaikwayo Da Ba Shi Da Tushe Na Japan Yana Yunkurin Shafa Wa Kasar Sin Kashin Kaji

October 29, 2026
’Yansanda Sun Kama Tsohon Gwamnan Imo Rochas Okorocha A Abuja

Kotu Ta Tabbatar Da Rochas Okorocha A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Na Imo Ta Yamma

October 29, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.