Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta buƙaci ƴan jarida su riƙa yi wa ƴan siyasa tambayoyi tare da ɗora musu alhakin bayyana matakan da za su ɗauka wajen inganta walwalar ma’aikata gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Ƙungiyar ta jaddada cewa Nijeriya na buƙatar albashin da zai wadatar da ma’aikaci wajen biyan buƙatun rayuwa, ba kawai mafi ƙarancin albashi da ba ya iya biyan muhimman buƙatunsa ba.
Mataimakin Sakatare na NLC, Chris Onyeka, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, cikin saƙon fatan alheri da ya gabatar a taron ƙungiyar masu bayar da rahotannin ƙwadago ta Nijeriya (LACAN) karo na uku. Ya ce zaɓen 2027 da kuma tattaunawar sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa su ne muhimman damammaki na magance matsin tattalin arziƙin da ma’aikata ke fuskanta.
Onyeka ya bayyana cewa mafi ƙarancin albashi ba kyauta ba ce, illa kuɗin da ya kamata a biya ma’aikaci bisa aikin da ya yi. Ya gargaɗi gwamnati kan aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙi da ke rage darajar albashin ma’aikata da sunan daidaita tattalin arziƙi. Ya kuma buƙaci masu bayar da rahotannin ƙwadago su binciki manufofin tattalin arziƙin jam’iyyun siyasa tare da neman takamaiman alƙawura kan albashi, tsaron aikin yi da kariyar zamantakewa.
Ya kuma yi gargaɗin cewa yaɗuwar aikin wucin gadi (contract), da bunƙasar ayyukan da ake samu ta intanet da sauye-sauyen tsarin aikin gargajiya na iya raunana haƙƙin ma’aikata da ikon ƙungiyoyin ƙwadago na yin ciniki a madadinsu. Ya ce ci gaban fasaha bai kamata ya zama sanadin tauye haƙƙin ma’aikata, da rashin biyan albashi mai kyau ko hana su kariyar zamantakewa ba.
Bugu da ƙari, Onyeka ya buƙaci LACAN ta ƙarfafa rawar da take takawa a cikin Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Nijeriya (NUJ), yana mai cewa ƴan jarida na buƙatar ƙungiyoyin ƙwararru masu ƙarfi domin kare ƴancin yaɗa labarai da inganta yanayin aikinsu.
Ya kuma buƙaci ƴan jarida su guji yaɗa farfaganda ko bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba, tare da ba da fifiko ga matsalolin ma’aikatan wucin gadi, masu ƙaramin albashi da sauran masu rauni a cikin al’umma. Ya ce ya kamata sauye-sauyen tattalin arziƙi su inganta rayuwar jama’a, maimakon ƙara jefa ma’aikata da talakawa cikin wahala.














