A ranar 28 ga watan Oktoba, Masamine Ryuho, shugaban tashar talabijin ta TBS ta Japan, ya yi kokarin kare shahararren shirin wasan kwaikwayo na tashar mai suna “VIVANT” (zango na biyu), wanda ya ci zarafin kasar Sin a fili, yana mai bayar da uzurin cewa shirin na “labarin al’mara ne kawai” kuma “ba a yi shi da nufin tozarta wata kasa takamaime ba.”
Wannan mataki ya jawo karin kakkausar suka daga masu kallo, a ciki da wajen kasar ta Japan.Kamar yadda aka sani, a lokacin yakin duniya na biyu, sojojin Japan sun kai harin mamaye kasar Sin kuma suka aikata manyan laifuka na rashin imani ga bil’adama. Amma duk da haka, wannan wasan kwaikwayo ba wai kawai ya kirkiro da abin da ake kira da “kungiyar leken asiri ta kasar Sin ba,” har ma ya “dasa” hanyoyin azabtarwa da sojojin mamayar Japan suka taba amfani da su a baya kan mayakan turjiya na Sin, kamar yanke yatsu da caka wuka ko takobi, a cikin halaye ko dabi’un Sinawa, inda ta haka ne ya juya tarihin mai laifi da wanda aka azabtar.
Wannan ba “labarin almara” ba ne, shafa bakin fenti ne. Dabara ce ta rashin kunya a yakin jirkita kaifin tunani da masu tsattsauran ra’ayi na Japan ke yi a kan kasar Sin, kuma yana fallasa yunkurinta na bata wa kasar Sin suna ta hanyar abubuwa na al’ada da kuma yada ra’ayoyin nuna kiyayya ga kasar Sin.
Abin da ya kamata tashar TBS ta yi a yanzu shi ne, kada ta yi amfani da dabaru na yaudara wajen boye kurakuranta, amma ta fuskanci tarihi kai-tsaye, ta yi tuba ta gaskiya, ta dakatar da shirin talabijin din da abin ya shafa, sannan ta nemi afuwar al’ummar kasar Sin.
Tarihi ya riga ya bayyana karara cewa, duk wani yunkuri na wanke cin zarafi ko gurbata gaskiyar tarihi ba zai yi nasara ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














