Sojojin Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane shida da aka yi garkuwa da su bayan musayar wuta da wasu ’yan ta’adda a ƙaramar hukumar Wasagu ta Jihar Kebbi.
Lamarin ya faru ne a ranar 2 ga watan Satumba, 2026, bayan sojojin sun samu sahihin bayanin cewa wasu ’yan ta’adda sun shiga ƙauyen Mehinua da ke kan hanyar Wasagu-Ayu.
Bayan samun bayanan, sojojin sun tafi yankin domin fatattakar ’yan ta’addan da kuma ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
Sojojin sun yi arangama da ’yan ta’addan, inda aka yi musayar wuta sosai.
Sojojin sun yi amfani da ƙarfinsu a kan ’yan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Dukkanin mutane shidan an ceto su cikin ƙoshin lafiya.
Sojojin sun kuma ƙwato wata mota a yayin aikin.
Daga bisani, an miƙa mutanen da aka ceto da motar ga hukumominda abin ya shafa domin ɗaukar matakin da ya dace.
Aikin ya nuna muhimmancin samun sahihan bayanan sirri da kuma gaggawar ɗaukar mataki wajen yaƙi da garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.














